Shaikh Zakzaky ya yi Allah-wadai da wulaƙanta Alkur'ani a Sweden

MMS HAUSA
0

Daga Zailani Mustapha 

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi tir da Allah-wadai da yadda wasu mutane suka wulaƙanta Alkur'ani mai girma. 

Wannan bayani ya fito ne daga ofishin Shehin Malamin a wani saƙo da aka wallafa a shafin Facebook a ranar Asabar 1 ga Yulin 2023, inda Shehin Malamin ya ce tabbas abin da ya faru labari ne mara daɗi, kuma hakan ya raunata zuciyar al'ummar Musulmi da masu neman ƴanci a duniya. 

Shehin Malamin ya ƙara da cewa; abin da ya faru cin fuska ne ga Musulunci da Musulmi. Inda ya nemi dukkanin masu neman ƴanci a duniya da ka da su yi shiru kan lamarin nan. Kuma dole ne a hukunta waɗanda suka aikata hakan. 

Shehin Malamin dai ya fara da cewa; "wannan labari mara daɗi na cin zarafin Alƙur'ani mai girma a ƙasar Sweden, ya raunata zukatan dukkanin musulmi da masu neman 'yanci na duniya", inji sakon .

Ya ci gaba da cewa; "Tabbas kona Alƙur'ani mai tsarki ba wai cin fuska ne ga Musulunci da musulmi ba, cin fuska ne ma ga dukkanin addinan duniya da mabiyansu. Don haka, ya zama wajibi ga duk wani mai ƴanci da kada ya yi shiru akan wannan aiki". 

Ya karkare da cewa; "Mun yi Allah wadai da wannan mummunan aiki da waɗanda suka aikata shi kuma muna kira da a gaggauta hukunta su".
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top