Daga Bashir Muhammad Maiwada
Kungiyar Kwallon Kafa Ta Al Hilal Dake Saudiya Ta Gabatar Tayi Mafi Tsada Ga Mbappe Kan Euro €300m.
Tayin Ya biyo Bayan Da Kungiyar PSG tasa ka Dan wasan a kasuwa da nufin siyar dashi Sakamakon rashin Kara kwantiragi ga Kulob ta PSG.
Saidai a bangaren Dan Wasa Baya Da Sha'awar Komawa wata Nahiyar buga Kwallo Face Chigaba da Zama a kasashen Europe don Chigaba da Fafatawa.
Dan Wasan Ya bayyana Cewa Tun Yana yaro Yakeda Sha.awar Zama Dan Wasa a Kungiyar Kwallon Kafa Ta Real Madrid Dake Spain.
Yanzu haka dai Kungiyar Ta PSG na dakon Jiran Kulob din Real Madrid don jin nata tayin da Kuma shauran Kungiyoyin Kwallon Kafa dake Nahiyar Turai.
Shin Kuna Ganin Real Madrid Zasu iya wuce wannan Farashin Da Al Hilal Ta Sanya ? Kuma Kuna Mafarkin Dan Wasan Zai Cika Kuwa?