Farfesa Gwarzo ya naɗa mataimakin shugaban sabuwar Jami’ar Franco-British, Kaduna

MMS HAUSA
0

Kwamitin amintattu na Jami’ar Franco-British International University dake Kaduna, ta amince da naɗin Farfesa Abdullahi Muhammad Sabo a matsayin mataimakin shugaban sabuwar jami’ar.

Har zuwa sabon naɗin nasa, Farfesa Sabo ya kasance tsohon shugaban makarantar gaba da digiri na ɗaya ta Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijer dake Maraɗi.

Wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ne ya sanar da naɗin a lokacin da yake miƙa takardar naɗin ga Farfesa Sabo a ranar Laraba, 12 ga Yuli, 2023.

“A madadin kwamitin amintattu na jami’ar Franco-British International University Kaduna da kuma gamayyar jami’ar Maryam Abacha American University, ina mai gabatar muku da takardar naɗin ka a matsayin mataimakin shugaban sabuwar jami’ar na farko,” Farfesa Gwarzo ya ce.

A yayin da yake yi wa sabon mataimakin shugaban fatan samun nasarar wa'adinsa, Farfesa Gwarzo ya bayyana kyakkyawan fatansa cewa Farfesa Sabo zai sauke nauyin da aka ɗora masa bisa la'akari da ƙwarewarsa da gogewarsa.

Ya nemi sabon mataimakin shugaban Jami'ar da ya tabbatar da rashin uzuri dangane da cin zarafin jinsi a sabuwar jami'ar.

Farfesa Gwarzo ya bayyana naɗin Farfesa Sabo a matsayin wanda ya cancanta idan aka yi la’akari da irin ɗimbin gogewarsa da yake da shi a fannin ilimi.

Ya roƙi Allah maɗaukakin Sarki da ya yi ma sabon mataimakin shugaban jagora, ya kuma ba shi hikimar tafiyar da shugabancin sabuwar jami'ar zuwa babban mataki. 

Da yake mayar da bayani, Farfesa Sabo ya godewa wanda ya kafa jami’o’in hudu, wato Farfesa Gwarzo inda ya zabo shi ya kuma naɗa shi a matsayin wanda ya cancanta. Ya kuma yi alƙawarin tabbatar da ya sauke amanar da aka damƙa mishi. 

Idan za ku iya tunawa, a ranar Litinin, 15 ga watan Mayu, 2023, majalisar zartaswa ta Tarayya, a zamanta ta amince da kafa sabbin jami’o’i biyu, Jami’ar Franco-British International University, Kaduna da Jami’ar Kanada ta Nijeriya, Abuja waɗanda dukkanin su mallakin Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ne. 

Hakazalika, Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa (NUC) a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, 2023, ta ba da lasisin gudanar da aiki ga Jami’o’in biyu.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top