Farfesa Adamu Gwarzo: Mutum Ne Da Ya Cancanci Yabo

MMS HAUSA
0

Dukkanin addinai na duniya suna koyar da kyautata wa mutane. Aikata alheri wata alama ce da ba ta gogewa a cikin zuciyar mai karɓa. Na taɓa karanta cewa “zama mutumin kirki yana da lada” a cikin littafin Noel Streatfeild da aka rubuta a shekara ta 1936. A yayin da karin maganar Afirka ke cewa duk wanda ya shuka abu mai kyau ba shakka zai girbi mai kyau, hakika mutanen kirki sun cancanci yabo domin wasu su yi koyi da su.

Kasancewa mutumin kirki yana da ma’anoni daban-daban ta fuskoki mabambanta ga mutane da yawa. Mutumin kirki zai iya daukar ma’anar dukkanin wani mutum da yake saukakawa al’umma radadi, yake kuma taimaka musu wajen cimma burinsu ko kuma yake taimaka musu wajen cimma muradinsu.

Shiga sahun masu gina kasa nauyi ne da ya rataya a kan wuyan dukkannin ‘yan kasa amma mutanen kirki ne kawai suke yin hakan. Gina kasa na da bukatar abubuwa da yawa daga kowanne dan kasa. Za mu iya sanya al'ummarmu ta zama abin da muke so idan har dukkanninmu muka hada hannu da karfe wajen ba da gudummawa ga bukatunta. Da ‘yar gudunmuwar da kowa zai iya bayarwa; za mu iya yin tasiri a rayuwarmu da na wasu. Wani abu mai kyau da ya kamata mu yi wa ƙasarmu a yanzu shi ne taimaka wa mutane domin biyan bukatunsu na ilimi.

Ilimi yana da matukar kimar da ba shi da farashi, sai dai wadanda suka fita daban ne kawai suke bayar da gudummawa wajen ci gaban ƙasa da ci gaban ɗan Adam, ba tare da mutane sun zama masu yanke kauna, shiga cikin rashin tsaro da zai dabaibaye su tare da hauhawar tashin hankali ba kamar tuddai. Mutanen da ke ba da ilimi, masu taimakon al’umma ne; ana kiransu da masu jin kai, domin Allah ne kadai zai iya sakawa irin wannan sadaukarwar da suke yi, ko da kuwa ana biyan masu makarantun kudi, su kuma suna biyan gwamnati da al’umma da kasa baki daya ta kowane fanni. Makarantun da suke ginawa suna samar da ayyukan yi, suna taimakawa gwamnati a nauyin da ya rataya a wuyanta na samar da ilimi, sannan mafi muhimmanci; masu makarantun suna biyan kudaden shiga kuma suna samar da aikin yi ga ‘yan ƙasa.

Farfesa Adamu gwarzo; matashin Farfesa ne a Arewacin Nijeriya daga jihar Kano wanda ya zama ginshiki ne na sabon ilimin zamani na Nijeriya tare da himma wajen taimakawa da samar da tsarin ilimi da ake da bukata a duniya. Tare da ƙwarewar da yake da shi a matsayinsa na Farfesa, kuma ɗan jarida, mai gudanarwa sannan hamshaƙin ɗan kasuwa, ƙoƙarin Gwarzo wanda ba ya gajiyawa ya kawo sabon tsari a Afirka. Gwarzo dan kasuwa ne na ilimi wanda gudunmawarsa a duniya ta sauya yanayin akidar ilimi a Afirka.

Tare da kafa Jami'ar Maryam Abacha American University (MAAUN) a Maradi dake Jamhuriyar Nijar da wata jami'a a Togo, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya kafa kyakkyawar tubali a fannin ilmantarwa a Afirka.

Tare da sha'awarsa da himmarsa wajen haɓɓaka ilimi domin biyan buƙatun aikin yi na zamani a cikin harsuna daban-daban; jajircewar Gwarzo ya sake farfado da wani fata ga 'yan Nijeriya na kafa wata jami'ar Amurka a Kano, domin cika bukatar dalibai da ka’idojin aikin yi a duniya. Jami'ar tana ba da darussa fiye da 15.

A kwanan nan, a wani labarin kuma, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta hannun Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC) a ranar 9 ga watan Yuni, 2023, ta bayar da lasisin gudanarwa ga Jami’ar Canada ta Nijeriya da ke Abuja da Jami’ar Franco-British International University, dake Kaduna wanda dukkaninsu mallakin Farfesa Adamu Gwarzo.

Jami’ar da ta yi fice ta farko a Nijar, dake Maradi ita ce kan gaba wajen sauya tsarin ilimin Afirka domin dacewa da tsarin ilimi na karni na 21 ta hanyar hada harsunan koyarwa da karatu. Jami'ar da aka ba wa sunan matar tsohon shugaban Nijeriya a tsakanin Nuwamba, 1993 - Yuni, 1998 (Marigayi Janar Sani Abacha), Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN), a Maradi ita ce jami’a mai zaman kanta ta farko a duk faɗin Afirka da aka kafa domin faɗaɗa harsunan duniya masu tsada a cikin ƙasashen Afirka tare da sabbin hanyoyin koyarwa.

Nasarorin da Farfesa Adamu Gwarzo ya samu ba wai kawai na fadada ilimi ne a Afirka ba, illa karamcinsa na kawo nesa a kusa tare da taimaka wa mutane wajen ganin sun cimma burinsu na ilimi da kuma taba rayukan miliyoyin mutane ta hanyar gidauniyarsa.

Tare da dimbin miliyoyin masu neman shiga jami’o’i a Nijeriya; Adamu Gwarzo ya rufe gibin tsallakawa jami'o'in kasashen waje. Kokarinsa na kashe tarin dalolin Amurka domin taimakawa ilimi, marasa karfi, mata tare da rage tasirin sauyin yanayi yana kawo sauyi a Afirka. Burinsa shi ne inganta ilimi, sha'awarsa ita ce cike fatan UNESCO da kuma tsarin ci gaba mai dorewa (SDGs) a Afirka.

Ta hanyar gudunmawarsa mara yankewa da yake bayarwa ga ilimi; Farfesa Gwarzo yana da lakabi da yawa na nuna godiya gare shi, an rubuta sunansa da ruwan zinare domin tunawa da shi na har abada, kuma Allah ya albarkace shi bisa irin sadaukarwarsa. Shugaban jami’o’in masu zaman kansu a Nijeriya ya samu yabo da dama da suka hada da wanda ya jagoranci samar da jami’o’in harsuna biyu a Afirka, da lambobin yabo na Sarautun gargajiya da dama da kuma lambobin yabo na kasa da kasa.

Gidauniyar Adamu Gwarzo ta zama hanyar rage radadi ga mutane, ta hanyar gidauniyar ana kashe miliyoyin kudade domin biyan bukatun jama'a da kuma kawo taimako ga kasashen Afirka. Taimakon da yake bayarwa ga ilimin Nijeriya yana da matukar muhimmanci da kowa ke iya gani kuma har ya shaida irin wannan taimakon jin kai da Gwarzo ke bayarwa a Afirka.

A shekarar 2021, Gidauniyar Adamu Gwarzo ta ba da gudummawar mota kirar bas mai cin mutane 66 na alfarma wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 50 da kuma motar daukar marasa lafiya ta Naira miliyan 20 ga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano Wudil (KUST). Haka kuma gidauniyar ta bayar da kyautar mota kirar bas mai cin mutane 60 ga Kaduna Polytechnic, haka zalika, gidauniyar ta bayar da kyautar motar alfarma mai kujeru 66 da kudinta ya kai Naira miliyan 50 ga jami’ar Al-Istiqama dake Sumaila ta jihar Kano. Sannan gidauniyar  ta Gwarzo ta bayar da tallafin motocin bas masu kujeru 60 na Mercedes-Benz ga jami’ar Bayero da ke Kano da kuma jami’ar gwamnatin Nijar.

Baya ga haka, bisa sha'awar da yake da shin a tallafawa wajen buga littattafai, gidauniyyar Adamu Gwarzo ta tallafa wa buga littattafai guda biyu da kudi har naira miliyun biyu. Littafan sune; “Pantami: The Trials and Triumphs of a Digital Economy Maestro,” na Mal. Yushau Shuaib da kuma “eNaira Revolution: A Peep into Nigeria’s Cashless Future,” wanda Mista Abdulrahman Abdulraheem ya rubuta. A shekarar 2022, Gidauniyar Gwarzo ta bai wa mata marasa karfi 100 na jihar Kano tallafin naira dubu hamsin (N50,000) ga kowaccensu. A shekarar 2022, Gidauniyar Gwarzo ta ba da tallafin Naira Miliyan 1 ga dalibin Nijeriya da yake karantar fannin likitanci da ya makale a kasar Rasha.

Tausayin Farfesa Adamu Gwarzo ba ya aunuwa kuma duk yana yin wannan ne saboda Allah da kuma ci gaban Afirka. A watan Yuni Gwarzo ya bai wa wani jami'in tsaronsa kyautar gida bisa gaskiya da rikon amanarsa. Gwarzo yana tausaya wa talakawa, yana taimakon marasa karfi, yana kuma kwantar da hankalin mutane ba tare da la’akari da kabilarsu, yankinsu ko addininsu ba. Ana ɗaukarsa a matsayin mutum mai ban mamaki wanda hangen nesansa shi ne gina al’umma ta kowanne fanni. Tabbas shi mutum ne da Allah ya yi a Nijeriya domin ya kawo ci gaba, ya kuma warware matsaloli da kuma koma bayan ilimi tare da kawo sauyin yanayi a Afirka, da wadannan, Farfesa Adamu Gwarzo ya cancanci yabo da addu'a.

Auwal Ahmed Ibrahim malami ne a Kaduna Polytechnic, a sashen Mass Communication, kuma ana iya samunsa ta auwalahmed@kadunapolytechnic.edu.ng
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top