Shahararren me kuɗin duniyarnan mamallakin manhajar Tuwita Elon Musk, ya ce zai sauya tambarin Tuwita daga Tsuntsu zuwa alamar 'X'.
A wasu jerin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na Tuwitar ranar Lahadi, Musk ya ce 'Ina son wannan, amma alamar 'X' ya fi'.
Yace sauyin tambarin zai bashi damar banbance kansa (kamfanoninsa) daga ragowar kamfanoni.
Tuni dai mutane suka fara baiyana ra'ayoyinsu game da kudirin, wanda Musk yace wataƙil zai fara aiki a daren yau (Lahadi) kafin ya baiyana baki ɗaya a wannan Litinin.