Farfesa Gwarzo Na Son Gwamnatin Jihar Kano Ta Sanyawa Makaranta Sunan Marigayi Haruna Abdullahi Gwarzo Domin Karrama Sa

MMS HAUSA
0

Wanda ya kafa rukunin jami’o’in Maryam Abacha American University ta Nijeriya da Nijer, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf da ta sanya wa wata makaranta sunan marigayi Haruna Abdullahi Gwarzo.

An yi wannan kiran ne a wata tattaunawa da ya yi da ‘yan jarida jim kadan bayan kammala ziyarar ta’aziyyar da ya kai ga iyalan mamacin a gidansu da ke Zango Quarters a jihar Kano.

 “Bukatarmu shi ne muna kiran wannan gwamnatin na Abba Kabir Yusuf ta karrama shi. Ta nemi wata makarantar firamare ko Sakandare a Gwarzo ta sanya sunan Marigayi Malam Haruna Abdullahi Gwarzo bisa gudummawar da ya bayar wajen ci gaban ilimi. Yana daga Malamai na farko-farko. Yana da kyau gwamnati ta karrama shi ya zama duk lokacin da iyalinsa suka duba za su tabbatar da cewa gwamnati ta yabawa gudummawar da mahaifinsu ya bayar”, inji Farfesa Gwarzo.

Marigayi Malam Haruna Abdullahi shi ne mahaifin Dr Murtala Haruna, Shugaban makarantar kimiyya da kimiyyar lafiya na Jami’ar Maryam Abacha American University.

Marigayin, mai shekaru 85, ya rasu ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) bayan ya sha fama da jinya.

Farfesa Gwarzo ya ce rasuwarsa babban rashi ne, ba ga iyalansa kadai ba, har ma ga daukacin al'ummar jihar Kano da Nijeriya baki daya. Ya kuma bayyana marigayin a matsayin mutum mai rikon amana, mai gaskiya, kwazo, da jajircewa.

“Mutuwa tana da zafi. Wannan rashi ne. Mun yi rashin babban Uba. Saboda a gida idan aka rasa Uba kamar an rasa wani bango ne, kafin ka samu wanda zai maye gurbin Uba ba karamin aiki bane. Malam Haruna mutum ne mai gaskiya da rikon amana. Wannan rashi ne ga al’ummar Gwarzo da jihar da ma Nijeriya baki daya.

Ya kuma bayyana marigayin a matsayin uba kuma kwararren mai ilimi wanda ya ba da gudunmawa sosai wajen bunkasa ilimi a Gwarzo, jihar Kano da ma kasa baki daya.

“Malam mutumin kirki ne, mutum ne da ya yi zaman bada ilimi, kuma duk mutumin da ya zaman bayar da ilimi tarihinsa ba ya taba karewa. Saboda yanzu haka ga dalibansa ana nuna mana. Duk mai ilimin da ya bayar da ilimi rayuwarshi ba ta karewa. Rayuwarshi na nan saboda shima ya ba wani ilimi. Shima wannan ya sake ba wani ilimi, to tarihi ba ta taba mantawa da wanda ya ba da ilimi ba”, inji shi.

Ya kuma bukaci iyalan marigayin da su yi koyi da mahaifinsu wajen rike wannan tarihin na bayar da ilimi, wanda a cewarsa bai kamata a daina ba, domin ya ce marigayin yana da mutane da yawa a matsayin dalibansa wadanda kuma suke koyar da al’umma masu tasowa ilimi.

“Yana da kyau iyali su hada kansu su yi koyi da abin da ya bari wanda za su ci gaba da yi ma al’umma. Abubuwan da ya yi ma al’umma suma su koya su ci gaba da yi ma al’umma. Saboda idan aka ce mahaifinka mutumin kirki ne, yana da kyau duk inda aka ganka a tabbatar da ka gaji halayen kirkin. Muna fata ‘ya’yansa da ya bari su yi koyi da halayen Malam”, ya shawarce su.

Daga karshe Farfesa Gwarzo ya yi addu’ar Allah madaukakin Sarki ya jikan Marigayin ya kuma sanya shi a Aljannar Firdaus, sannan ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure rashin da ba za a iya maye gurbinsa ba.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top