A Karo Na Uku Makarantar Fudiyyah Samaru Ta Yi Walimar Saukar Karatun Alkur’ani Na Dalibai 27

MMS HAUSA
0

Daga Muhammad A. Dalhatu

Da safiyar ranar Asabar 3 ga Yunin 2023 daidai da 14 ga Zulkadah 1444, makarantar Fudiyyah Samaru wanda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya rushe gab da sauka mulkinsa, ta yi walimar yayen dalibanta 27 da suka yi saukar Alkur'ani mai girma.

Walimar saukar daliban wanda ya hada maza 13 da mata 14, ya samu halartar al’umma daban-daban daga sassan Zariya da kewaye.

Bikin yayen shi ne karo na uku, inda aka soma da bude shi da addu'a wanda Alaramma Alfa ya yi. Sannan Nusaiba Musa da Mahdi suka gabatar da jawabin maraba cikin harshen Larabci da Hausa. Sannan Mahdi Isa Waziri ya jagoranci daliban wajen gabatar da taken makarantar da ziyara.

Alhaji Mansur Aliyu shi ne ya gabatar da jawabin gabatarwa, inda ya nemi iyaye da Malaman makarantar a ci gaba da bayar da ilimi cikin tsoron Allah domin ci gaban makarantar. Ya kuma bayar da tabbacin cewa rushe musu makaranta ba zai hana su ci gaba da ilmantar da 'ya'yansu ba. Kuma kamar yadda aka rusa musu suka gina, haka zalika za su sake gina makarantar ta su. Ya kuma karfafa daliban a kan ci gaba da karatunsu na hadda da kuma littafai.

An kuma gabatar da kasidu cikin harsunan Larabci, Turanci da kuma Hausa wanda shima daliban suka gabatar kan ilimin Alkur'ani mai girma. Daliban da suka jagoranci wannan sun hada da Firdausi Bashir, Khadija Idris, da kuma Zulaikhat Abdulhamid.

Bayan nan, Husaini Mansur Aliyu, daya daga cikin Malaman makarantar ya jagoranci daliban da suka yi saukar wajen gabatar da su daya bayan daya domin su yi karatun Alkur'ani mai girma.

Bayan daliban guda 27 sun kammala karanto ayoyin Alkur'ani mai girma, wakilin ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky na Samaru, Malam Barau ya gabatar da babban Malami mai jawabi, Shaikh Abdulhamid Bello domin gabatar da jawabin rufewa. Cikin jawabinsa ya soma da taya daliban murnar saukar Alkur'ani mai girma, sannan ya karfafa su akan cewa su sa a ransu cewa yanzu suka soma karatu.

Sannan ya lurantar da muhimmancin koyi da Alkur'ani, inda ya ce littafi ne da ya kasance alheran komai da komai, kuma shi ne mafitar al'ummar nan. “a sanya Alkur’ani a gaba, a yi aiki da shi. Alkur’ani shi ne alami na gaskiya, shiriya, adalci, alkhairi, tsira da komai ma”, ya tabbatar.

“don haka yanzu kun fara digon Ba ne wajen karatu, saboda haka ku karfafa karatun. Abu na biyu kuma shi ne kokarin aikata abin da aka karanta. Saboda ilimi ba wani abu bane face aiki da shi. Kuma dama manufar sauko mana da Alkur’ani da Allah ya yi domin ya kasance shiriya ga tafiyar da rayuwarmu baki daya. Ba kawai mu yi karatu domin a ce mana Alaramma ko Shehi ko mu samu satifiket mu kama aiki kawai ba. Alkur’ani ko ma wani iri nau’i na ilimi ga shi ma’abocin Alkur’ani shi ne ya zamo masa hanyar tsira duniya da lahira”.

Har wala yau Shehin Malamin ya kawo Hadisin Manzon Allah dake nuni da cewa ku koyar da 'ya'yanku abubuwa uku; son Manzon Allah, son iyalan gidansa da kuma karatun Alkur'ani inda ya karfafa kan hakan. “Iyaye tun yaro na karami a nuna masa wane ne Manzo Muhammadu (S) domin ya so shi. Wane ne kuma Ahlul Baiti (AS) a sanar da su dukkannin Imamai din nan sha biyu, sannan kuma a nuna musu wajibi ne sanin su da son su da yin koyi da su. Sannan kuma da karatun Alkur’ani. A dunkule za mu iya cewa da Alkur’ani da Manzon Allah (S) zamu iya cewa da Imamai abu guda suke. Bangarori biyu ne na abu guda daya. Ba zai yiwu ka yi riko da Alkur’ani ka yi watsi da Manzon Allah (S) ba. Ba zai yiwu ka yi riko da Manzon Allah ka kuma ce ba ruwanka da Alkur’ani ba”, ya lurantar.

A karshe ya ce matsalolin da al'umma ke ciki a yanzu, to mafitarsu na ga Alkur'ani wanda koyi da karantarwarsa ne kadai zai fisshe da al’umma duniya da lahira, inji shi.

Bayan ya kammala jawabinsa, an gabatar da shaida ga daliban da suka yi saukar da kuma Malamansu. Daga nan Malam Lukman Alfa ya gabatar da jawabi a madadin Malamai da dalibai. Shi kuma Injiniya Lawal ya gabatar da jawabin godiya. Daga karshe Shaikh Abdulhamid Bello ya rufe taron da addu'a.

A yayin zantawarmu da daliban duk sun nuna farin cikinsu da godiya ga Allah da ya nuna musu wannan rana, inda suka ce yanzu ne ma za su dora dambar soma karatu. Inda suka yi kira ga matasa takwarorinsu da su dage su nemi ilimi, domin ilimi haske ne.


Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top