Shugaban NUC Ya Kaddamar Da Tagwayen Ginin Da Aka Sanya Wa Sunansa A Jami'ar MAAUN Kano

MMS HAUSA
0


Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC), Farfesa Abubakar Adamu Rasheed a ranar Litinin ya kaddamar da manyan tagwayen ajujuwan karatu da aka sanya wa sunansa a Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano. 

Farfesa Rasheed wanda ya kaddamar da ginin, ya bayyana jin dadinsa da irin kayayyakin da ya ga an tanada a ajujuwan, sannan ya mika godiyarsa ga hukumar gudanarwar jami’ar da ta sanya wa tagwayen ajujuwan sunansa. 

Ya yabawa wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa ta MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen daukaka darajar ilimi a Nijeriya da ma sauran kasashen duniya. 

Bayan kaddamar da ginin, an zagaya da Farfesa Rasheed wasu wurare a cikin Jami'ar da suka hada da dakin karatu na Murtala Ramat Mohammed, dakin wasanni na Ibrahim Usman Yakasai da kuma makarantar kimiyyar lafiya.

A yayin taron, Farfesa Rasheed ya samu rakiyar Farfesa Gwarzo, Mataimakin Shugaban jami’ar MAAUN bangaren gudanarwa, Dakta Habib Awais Abubakar, Mataimakin Shugaba bangaren lura da rayuwa a jami'ar, Dakta Hamza Garba da Farfesa Ibrahim Usman Yakasai. 

Sauran sun hada da shugaban sashen makarantar zamantakewa da kimiyyar gudanarwa, Dr. Mahmoud Muktar Sa'id da mataimakin shugaban jami’ar bangaren sha'anin kudi, Mista Dauda Abdulrazaq Kayode da dai sauransu.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top