Mutanen Arewa Mazauna Legas sun nuna Bola Ahmad Tinubu a matsayin wani mutum mai kaifin hankali da zai magance matsalolin tsaron da suke addabi wannan ƙasar musamman yankin arewa
A ranar Lahadi din da ta gabata ne, yan arewa mazauna Legas suka jadadda amincewa da nuna goya wa takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar APC a zaɓe mai zuwa.
Haka kuma sun ɗauki alƙawarin aiki tukuru domin ganin ya sami nasara a wannan kakar zaɓe ta shekarar 2023 sun kuma amince da takarar gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu wanda ke neman waadi na biyu na shugabancin jahar Legas.
A yayin da yake ayyana wannan goyon baya ga 'yan takarar guda biyu a filin wasa na Mobolaji Johnson da ke Onikan,shugaban kungiyar 'yan asalin arewacin Najeriya mazauna jihar Legas na jam'iyyar APC Alhaji Sa'adu Yusuf Gulma Ɗandare ,ya bayyana cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi ayyuka masu yawan gaske a Legas da Najeriya inda ya ƙara da cewa idan Najeriya ta yi da cen samun mutane kamar Bola Ahmed Tinubu ci gaban da za ta samu gagarumi namiji
Alhaji Sa,adu Yusuf ya ƙara bayyana cewa amincewa da Asiwaju Bola Ahmed ya sami sahalewar dukkan ‘yan arewa mazauna Legas waɗanda suka yarda da cancantar sa da kuma ganin shine zai iya haɗa kan dukkan ‘yan Najeriya a matsayin tsintiya- madaurin ki- daya ba tare da nuna banbancin kabila ko adddini ba.
Haka kuma Bola Ahmed Tinubu ya kasance cikakken ɗan Najeriya mai kishin ƙasa wanda ba ya aiki da la'akari da banbanci addini da ƙabilanci ko wurin da mutum ya fito.
Lokacin da ya ke gwamnan a jihar Legas ya baiwa mutane da suka fito daga ɓangarorin da dama na Najeriya muƙamai a jihar ba tare da la'akari da inda suka fito ba inji Alhaji Sa'adu Yusuf.
Shugaban na ‘yan arewa mazauna jihar Legas ya kuma ƙara zayyana yadda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sanya harsashin da ya tabbatar da kyakkyawar zamatakewa ga 'yan Najeriya a jihar Legas ba tare da wata tsangwama ko cikas ba.
"A bisa yadda Bola Ahmed Tinubu ya haifar da ci gaban da ba a taɓa gani ba a jihar Legas ta fuskar ayyukan gwamnati da gine gine-gine a Legas, akwai buƙatar a bashi dama ya gudanar da irin waɗannan ayyuka na alheri ga Najeriya baki ɗaya."
A Saboda haka ne Alhaji Sa'adu yake ganin akwai buƙatar su tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓe mai zuwa ganin irin shugabancin sa mai nagarta da kuma sha'awar da yake da ita a bisa al'amurra na ci gaba da suka shafi 'yan arewa mazauna kudu masu yammacin Najeriya'
"A yau muna alfaharin fitowa fili domin nuna goyon baya ga wannan babban ɗan kishin ƙasa wanda ya sadaukarwarsa da kishin ƙasar da kuma jajircewar sa akan abubuwan da suka shafi ci gaban 'yan arewacin Najeriya da kuma 'yan ƙasa baki ɗaya ba shi da na biyu" inji Alhaji Sa'adu
Alhaji Sa'adu yana shawartar shuwagabannin 'yan arewa mazauna Legas kuma mutanen arewa a dukkan faɗin Najeriya ,musamman masu ƙaramin karfi ,matasa da mata da su yi watsi da ɗabi'ar nan ta karɓar ɗan wani abu da bai taka kara ya karya ba, su yi gwanjon rayuwar su ta gaba maimakon haka su zaɓi Bola Ahmed Tinubu wanda zai inganta rayuwar su da kuma samarwa matasan su rayuwa mai inganci.
A cewar sa Tinubu ya hakikance cewa akwai alaƙa tsakanin dattijai da matasa a saboda haka yana tare da matasa da magabata a koda yaushe. Babu shakka mutanen arewa mazauna Legas na ganin Bola Ahmed Tinubu a matsayin babban abokin tafiya ɗan uwa haka kuma wani babban abin koyi ta fuskar shugabanci na gari.
A na sa ɓangare gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce Najeriya ta kunshi ƙabilu da dama Bola Ahmed Tinubu kuma ya sha nuna zai ya amfani da banbance banbancen da ke akwai a Najeriya domin haifar da cigaba da haɓakar tattalin arziki.
"shine ya kamata 'yan arewa su kaɗawa kuri'a domin Tinubu ne babbar alama ta haɗin kan Najeriya ,kuma shi ne ya kamaci zama shugaban ƙasa gwamnan na jihar Kano ya ce.
A yayin da yake nuna jin daɗin kalaman da aka furta ɗan takarar jam'iyyar ta APC na shugabancin Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa Alhaji Sa'adu Ɗandare a matsayin shugaban APC na 'yan arewa mazauna jihar Legas ya kuma ce a lokacin da ya ke hwamnan jihar Legas ya zaɓi mutane daga dukkan faɗin Najeriya a matsayin jami'an na gwamnati da suka yi aiki tare.
"muna tare da Yarabawa 'yan ƙabilar Igbo da 'yan arewa ƙabilanci ba shi ne abu mai muhimmanci ba a gare ni to amma cancanta ka da kuma ci gaban da za ka samar ga mulkin al'umma shi ne abu mafi muhimmanci a gare ni" inji Bola
A bisa abubuwan da ya tanadarwa Najeriya da kuma arewa,Tinubu ya yi alakawarin magance matsalar tsaro a dukkan fadin kasa,inda ya bayyana cewa tattalin arzikin kasa ba zai habaka ba a inda babu tsaro.
"Idan har 'yan Najeriya suka zaɓe ni a matsayin shugaban ƙasa abin da zan bai wa fifiko shi ne samar da tsaro a ƙasa da kuma tabbatar da haɓakar tattalin arziki na jama'a sannan zan kirkiri tsare-tsare da cibiyoyi na warware ƙalubalen da Legas ke fuskanta zan ƙara yawan jami'an tsaro in kuma ba su kayan aiki. Kazalika zan ƙara samar da na'urori na sanya idanu ta sama da ƙasa domin gano maɓoyar bata gari da kuma yakar su har sai an gama da su" inji shi
Sanata Bola Ahmed Tinubu ya kuma yi alƙawarin samar da ayyukan yi ga matasa da ƙara samar da wutar lantarki domin baiwa jama'ar ƙasa dama su fara ƙananan sana'o'i domin ciyar da iyalan su.
Bola Ahmad Tinubu ya kuma ce zai baiwa aikin gona kulawar gaske domin ƙara samar da abinci da samar da kuɗin shiga ga manoma da dawowa da darajar noma.
Ya ce zai sanya jari mai yawa wajen gina sabbin tituna da hanyoyi na jiragen kasa domin saukin sufuri na kayayyaki da kuma karfafa bangaren ilimi saboda inganta rayuwar matasa ta gaba.
Haka kamu zamu sanya jari a rijiyoyin mai na Kolmani wanda shugaba Buhari ya ƙaddamar, haka kuma zamu sanya jari a ayyuka masu muhimmanci kamar tashar samar da wutar Lantarki ta Mambila da kuma aikin bututun gas na AKK.
Idan aka farfaɗo da hanyoyin ruwa na cikin gida ta hanyar yashe kogin Naija da kuma rage shigo da karafa ta fuskar farfaɗo da kamfanin karafa na Ajaokuta Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ƙara da cewa.
A cikin waɗanda suka halarci wannan taro har da tsohon gwamnan jihar Bauchi Alhaji M.A Abubakar.