Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bukaci daukacin Sarakuna da masarautun jihar da su yi kokarin samar da zaman lafiya da hadin kai da shiga ayyukan al’umma domin kawo ci gaba mai dorewa.

Gwamnan ya bayar da wannan shawarar ne a yayin bikin nadin Sarauta da kuma mika ma Sarkin Gwantu sandar soma aiki. Bikin nadin sarautar na Mai Martaba Sarkin Gwantu, Alhaji Balarabe Abdullahi Karma an gudanar da shi ne a Gwantu dake karamar hukumar Sanga a kudancin Kaduna.

Tunda fari a cikin jawabinsa, gwamnan ya fara ne da cewa, “Ku ba ni dama na fara da taya al’ummar masarautar Gwantu wadanda lokuta da dama suka bayyana mana farin cikinsu kan yadda aka sake fasalin tsohuwar masarautar Gwantu wanda ya yi sanadiyyar samar da masarautar Arak. Gwantu tana da tsohon tarihi na tsawon shekaru fiye da dari, wanda gwamnatin jihar Kaduna ta sake kafawa domin gyara wasu matsalolin mulki.

“A don haka muna yi wa al’ummar wannan tsohuwar masarauta da Majalisar masarautar ta Gwantu fatan samun nasara wajen ganin ta kasance daya daga cikin Masarauta mafi kyau a jihar, ta samu zaman lafiya, hadin kai da kuma shiga ayyukan al’umma.” Inji Gwamnan.

“Muna taya Mai Martaba Alhaji Balarabe Abdullahi Karma murna bisa nadin da aka yi masa a matsayin Sarkin Gwantu mai daraja ta biyu, muna yi masa fatan alkhairi tare da yi masa addu’ar kammala sarautar Gwantu da aikin jihar baki daya lafiya. An daukaka matsayinsa inda aka dora masa wasu ayyuka masu yawa, wadanda suka wuce irin ayyukan da ake gani na sarauta", in ji shi

Da yake yabawa Sarakunan gargajiya bisa goyon bayan da suke bayarwa ta fannin tattara bayanan sirri domin shawo kan kalubalen tsaro a jihar da kuma adana bayanai, gwamnan ya kuma bukaci daukacin al’umma da masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tabbatar da kyakkyawar alaka da zaman tare, inda ya nemi kafatanin al’umma da su hadai kai domin tabbatar da an gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.

Gwamnan ya ci gaba da cewa; “A yayin da muke tunkarar zaben 2023, ina kira ga shugabanninmu na gargajiya, al’ummarmu da kuma malaman addininmu da su ci gaba da wa’azi domin tabbatar da an gudanar da ‘yancin dimokuradiyya cikin lumana, a kwadaitar da duk wadanda suka cancanci kada kuri’a su yi hakan cikin ’yanci, a cikin yanayin da babu tashin hankali ko tsoratarwa.

“Kada ’yan siyasa su yi amfani da matasan mu wajen tauye hakkin da tsarin mulki ya ba kowane dan kasa na zaben jam’iyya da dan takarar da yake so. A bangarenmu, gwamnati za ta tabbatar da ta bayar da tsaro domin bayar da damar da ‘yancin kada kuri’a ga masu zabe da yardar Allah,” in ji El-Rufai.

Da yake mayar da bayani, Sarkin Gwantu ya ce, “Ina so na tabbatar wa da mai girma Gwamna cewa, bisa ga salon mulkin ka, manufata ga masarautarnan shi ne tabbatar da tsaro, zaman lafiya, hadin kai da kuma mutunta al'adu da addinin juna.

“Wannan abu ne da kowa ya sani a duniya cewa; tsaro, zaman lafiya da hadin kai su ne ginshikan da ke tabbatar da ci gaban kowacce al'umma. A kan wannan tafarki ne ni, da mutanen masarautarnan za mu tsara matakan da za mu bunkasa rayuwarmu domin cimma wadannan muradan”.

An haifi Sarkin Gwamnatu a ranar 31 ga Maris, 1955 a Gwantu. Balarabe Abdullahi Karma, ya fito ne daga gidan mulki na “Gbatun”.

A farkon rayuwarsa Balarabe Abdullahi Karma ya sami ilimin addinin musulunci a garin Gwantu inda ya koyi Alkur'ani da koyarwar Annabi Muhammad (S). Daga baya ya fara karatunsa na firamare kuma ya kammala a shekarar 1969.

Ya yi digirinsa a bangaren tattara bayanai kan laburare da halayyar dan Adam daga Jami’ar Bayero dake Kano, inda ya kammala a 1988.

Karma wanda ya kasance Malami tsawon rayuwarsa tun daga matakin firamare har zuwa makarantar sakandare har ma ya zama shugaban Makarantar Sakandaren Gwamnati Gbonkok, Arak na farko.

A cikin 2002, aka canza masa wurin aiki zuwa Ofishin yanki dake Anchau a matsayin mai kulawa. Ya kai har matsayin Darakta a sashen tabbatar da inganci. Balarabe Abdullahi Karma ya yi ritaya daga aiki a ranar 31 ga Maris, 2015, bayan ya shafe sama da shekaru talatin da biyar (35) yana aikin gwamnati.