Shugaban Jami’ar Maryam
Abacha American University ta Nijer (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya
jajanta wa shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum bisa rasuwar surukarsa,
Hadjiya Bintou.
Hadjiya Bintou ta rasu
ne a ranar 29 ga watan Oktoba, 2022 a birnin Paris na kasar Faransa bayan
gajeruwar rashin lafiya.
Farfesa Gwarzo wanda
shi ne wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha
American University ta Nijeriya, da kansa ya mika sakon ta’aziyyarsa ga shugaba
Mohamed Bazoum a lokacin da ya ziyarci fadar shugaban kasar a Yamai a ranar
Laraba 16 ga watan Nuwambar 2022.
Farfesa Gwarzo, har
wala yau ya jajantawa shugaban kasar, gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Nijar, inda
ya bayyana rasuwar Hadjiya Bintou a matsayin babban rashi ba kawai ga danginta kawai
ba, har ma ga daukacin al’ummar Jamhuriyar Nijar.
“A madadin iyalina da Jami’ar
Maryam Abacha American University (MAAUN), muna mika sakon ta’aziyyarmu ga
shugaban kasa Mohamed Bazoum bisa rasuwar mahaifiyarmu, Hadjiya Bintou,” in ji
Farfesa Gwarzo.
Ya yi nuni da cewa
marigayiyar ta yi rayuwa mai cike da gamsarwa da kuma amfani wanda ya dace a yi
koyi da duk wadanda suka kusanci ta a lokacin rayuwarta.
Farfesa Gwarzo, wanda
kuma shi ne Shugaban Kungiyar Jami’o’i Masu Zaman Kansu ta Afrika (AAPU), ya yi
addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya bai wa Shugaban kasa Mohamed Bazoum da
matarsa hakurin jure rashin da ba za a iya mayarwa ba.
Ya kuma roki Allah
Madaukakin Sarki da Ya gafarta mata dukkan kurakurenta, ya kuma sanya marigayiyar a Aljannar Firdausi.
Da yake mayar da bayani,
shugaba Mohamed Bazoum ya godewa Farfesa Gwarzo bisa ziyarar ta’aziyyar da ya
kai masa, ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya saka masa da alheri.
Marigayiya Hadjiya
Bintou ita ce mahaifiyar Uwargidan shugaban kasa Mohamed Bazoum, kuma tuni aka
binne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a birnin Yamai na Jamhuriyar
Nijar.
Allah ya jikanta da Rahama
ya huta lafiya, amin.