Mun Dakatar Da Dukkan Wani Rubutu Akan Tinubu Har Sai Baba Ta Gani — Arewa APC Media

MMS HAUSA
0


Haɗaɗiyar Ƙungiyar nan ta 'Arewa Media Influencers ta sanar da dakatar da dukkan wani labari wanda ya shafi ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shattima har sai baba ta gani.

Kungiyar wanda ta fitar sanarwar yau a a ƙarƙashin shugaban na ta Malam Rabi'u Biyora, inda ƙungiyar ta ayyana dakatarwar sai baba ta gani saboda rashin adalci da ake yi ga Ƴaƴan ƙungiyar na ta tsawon lokaci.

“Insha Allah nan bada jimawa ba zamu sanar da mutane mataki ba gaba da zamu ɗauka, amma zuwa yanzu dai mun dakatar da dukkan wani abu da ya shafi ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin sa Kashim Shattima.” Inji Ƙungiyar.

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top