Farfesa Gwarzo Ya Jajanta Wa Shahararren Mawakin nan, Davido Bisa Rasuwar Ɗansa

MMS HAUSA
0


Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya jajanta wa shahararren mawakin nan, Davido bisa rasuwar dansa na farko, Ifeanyi.

Rahotanni sun ce Ifeanyi mai shekaru uku da haihuwa ya nutse ne a cikin wani wurin ninkaya da ke gidan mawakin da ke Unguwar Banana Island a Legas.

Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Gwarzo ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai a Kano a ranar Alhamis.

Farfesa Gwarzo, wanda shi ne wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, ya bayyana rasuwar Ifeanyi a matsayin abin ban tsoro idan aka yi la’akari da yanayin da yaron ya rasu.

“A madadin iyalina, Jami’ar MAAUN, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga Davido da matarsa bisa rasuwar dansu na farko, Ifeanyi,” in ji Farfesa Gwarzo a cikin sakon ta’aziyyar.

Farfesa Gwarzo wanda kuma shi ne shugaban kungiyar jami’o’i masu zaman kansu na Afrika (AAPU) ya yi amfani da wannan dama wajen jajantawa masoya da abokan mawakin, inda kuma yi addu’ar Allah ya bai wa iyalan marigayinhakurin jure rashin da aka yi.

Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top