Dr. Dauda Lawal Ya Maida Martani: Takardun Makarantana Ingantattu Ne, Ba Na Bogi Ba Irin Na Gwamna Matawalle

MMS HAUSA
0

Ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal ya mayar da martani mai zafi kan ƙarairayin da ake yaɗawa kan takardun makarantarsa da ya gabatarwa da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).

Lawal ya ce, takardunsa ingantattu ne kuma waɗanda ya same su ta halastacciyar hanya, ba irin na gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ba. Wanda a cewarsa, akwai ayoyin tambaya kansu.

A ‘yan kwanakin nan an samu wani labari da ya fito daga ɓangaren gwamnatin jihar Zamfara dangane da takardun da Dr. Dauda Lawal ya miƙawa hukumar INEC, inda suke cewa akwai bambance-bambance a sunayensa, da wurin haihuwa.

Sai dai a wata takardar sanarwar manema labarai wacce Ofishin Yaɗa Labaran Dauda Lawal ta fitar ranar Lahadi a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, Lawal ya ce, wannan lamarin ba komi ba ne face tsagoron jahilci da adawa irin na jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara da Gwamna Bello Matawalle.

“Irin wannan ƙarairayi da ƙazafi ba yau gwamnatin Matawalle ta fara yaɗa shi ba. Saboda a firgice gwamnan yake da irin farin jini da amsuwan da Dauda Lawal yake ci gaba da samu a faɗin Jihar Zamfara.

“A labarin da suka yi ta yaɗawa, sun ce Dr. Dauda Lawal ya gabatarwa da INEC da takardun makaranta waɗanda suke ɗauke da mabambantan sunaye, shekarun haihuwa, da kuma wurin haihuwa.

“Muna mayar da wannan martani ne saboda mu yi wa masoya da magoya baya ƙarin haske. Ko ba komi, Dr. Dauda Lawal takardun makarantarsa ingantattu ne, kuma ta halastacciyar hanya ya same su, ba kamar  yadda Gwamna Matawalle yake ta fama a kotu ba, saboda zargin da ake yi cewa dukkanin takardun karatunsa na bogi ne.

“A garin Guga daka Ƙaramar Hukumar Bakori ne aka haifi mahaifiyar Dr. Dauda Lawal. A matsayinsa na ɗan fari a wurin mahaifiyarsa ne ya sa bayan da aka haifeshi, sai kakansa ta ɓangaren uwa mai suna Alhaji Ado, ya ɗauke shi.

“Alhaji Ado, Kakan Dauda Lawal shi ne ya sanya shi a makarantar Firamare. Kuma bisa al’ada da tarbiyya irin ta mutanenmu, sai ya zama an yi wa Dr. Dauda Lawal rajista ne da suna ADO DAUDA. A wannan dalili ne ya sa satifiket ɗin kammala Firamare na Dauda Lawal yake ɗauke da sunan Ado Dauda.

“Bayan ya kammala Firamare, Kakansa Alhaji Ado ya kai shi makarantar Sakandare ta gwamnati dake Kachia a Jihar Kaduna. Shi ma a nan an yi wa Dauda Lawal rajista ne da suna Ado Dauda Lawal. Wanda a nan muna iya ganin sunan kakansa ta ɓangaren uwa, sunansa da kuma sunan mahaifinsa.

“Bayan ya kammala Sakandare, Dr. Dauda Lawal ya koma wurin mahaifinsa Alhaji Lawal, inda daga nan ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya don yin digiri. Takardarsa ta shaidar kammala digirin farko a fannin kimiyyar siyasa, wacce aka bashi a shekarar 1987 tana ɗauke ne da sunan DAUDA LAWAL. Haka nan kuma takardar shaidar kammala digirinsa na biyu a shekarar 1992, daga tsangayar kimiyyar siyasa, ita tana ɗauke ne da sunan DAUDA LAWAL.  Takardar shaidar bautar ƙasa (NYSC) wacce aka ba shi a ranar 17 ga watan Satumbar 1989, ita ma tana ɗauke ne da sunan DAUDA LAWAL.

“Wannan kaɗai ya isa ya nuna cewa, akwai kuskure wurin rubuta sunan Dauda Lawal a satifiket ɗinsa na Firamare da Sakandare. Da yake ɗan takarar gwamnan Zamfara na PDP, Dauda Lawal mutum ne mai bin dokoki da ƙa’ida. Bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya samu takardar rantsuwa daga Kotun Ƙolin Nijeriya, inda ya gyara sunansa, ya kuma gyara asalin jiharsa.

“Dr. Dauda Lawal ya samu takardar rantsuwa daga Kotun Koli ne a ranar 12 ga watan Satumbar 2018, inda ya bayyana cewa, ingantaccen sunansa shi ne Dauda Mohammed Lawal, kuma shi ɗan asalin Gusau ne a Jihar Zamfara.

“Wannan ya bayyana komi a fili dangane da bambancin sunan da ke jikin takardun Dauda Lawal. Babu wani abu da yake ɓoyewa, ko ya yi a ɓoye. Zai iya kare dukkanin takardunsa a ko ina ne, ba kamar yadda ake ta tataburza da Gwamna Matawalle ba, ya kasa bayyana inda ya samo takardar ‘Technical Certificate’ ɗin da yake yawo da shi, haka nan kuma ya kasa bayyana ingancin satifiket ɗin NECO ɗin da gabatarwa INEC a matsayin shaidar kammala karatun Sakandare.”

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top