Harkar Musulunci Ta Nemi Kotu Ta Jefa Sufeto-Janar na Ƴan Sanda Gidan Yari

MMS HAUSA
0


Harkar Musulunci wanda Shaikh Ibraheem Zakzaky yake ma jagoranci ta sha alwashin ci gaba da fuskantar sabbin kararraki guda bakwai da za ta gurfanar da Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba da sauran su bisa zargin kashe ‘ya’yanta, yayin da suke gudanar da zagayen juyayin Ashura a jihar Kaduna.

Kungiyar ta yi wannan alkawarin ne a cikin wata sanarwa da Dakta Dauda Nalado ya raba wa manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata tare da mika wa manema labarai a madadin Dandalin Academic Forum na Harkar Musulunci a Abuja.

Almajiran Shaikh Zakzaky sun jaddada cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai an yi adalci a kararrakin da aka shigar a sashin shari’a na Kaduna na babbar kotun tarayya.

“Muna sanar da jama’a cewa an shigar da kararraki bakwai kan Sufeto Janar na ‘yan sandan kasa (IGP) da wasu mutane 5 kan kisan gillar da aka yi wa masu juyayin Ashura bakwai a cikin garin Zariya.” Inji shi.

Za a iya tunawa lambobin kararrakin sun hada da: FHC/KD/CS/135/2022 tsakanin Aliyu Badamasi vs IGP da wasu 5;  FHC/ABJ/CS/145/2022 tsakanin Bashir Lawal Vs.  IGP, Mataimakin Sufeto-Janar (AIG) na ’yan sanda shiyya ta 7, Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna, Daniel Pom tsohon mai rike da ofishin ƴan sanda na Dibishin ɗin Soba, da dai sauransu.

An shigar da karar mai lamba: FHC/KD/CS/135/2022, a cewarsa, an shigar da karar ne a ranar 26 ga Satumba, 2022.

“Jama’a za su iya tuna cewa a ranar 8 ga watan Agusta, 2022, tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin kwamandan ‘yan sandan yankin Zariya na rundunar ‘yan sandan Nijeriya tare da DPO na Kasuwan Mata Sabon Gari da Zariya sun bude wuta kan musulmin da suka  gudanar da muzaharar lumana domin tunawa da ranar Ashura a Zariya.

“Harin na ba bisa ka’ida ba ya kai ga kashe mutane bakwai da suka hada da: Muhsin Badamasi, Muhammad Yusuf, Kazim Umar, Auwal Mustapha, Umar Inuwa, Aliyu Lawal da Jafar Magaji,” Nalado ya nunasshe.

Ya ce wadanda suka shigar da karar suna rokon kotun ta bayyana cewa harbi da kashe wadannan mutane bakwai a lokacin da suke gudanar da Ibadar su a matsayin Haramtaccen kisa kuma babban take hakkinsu na rayuwa ne da ‘yancin walwala.

“sannan an kuma gurfanar da wasu kara guda hudu a kan Sufeton da kuma wasu mutane 3 da ake zargi da kai hari tare da kashe mabiya Shi’a hudu (4) da suka hada da, Zaharaddeen Lawal, Aminu Abdulkadir, Mubarak Iliyasu da Musa Adamu.

‘Yan sanda sun kashe wadanda abin ya shafa ne a lokacin da suke gudanar da ibadarsu da suka hada da jerin gwanon juyayin Ashura a garin Soba na Jihar Kaduna a ranar 28 ga Agusta, 2022.

"Tsohon DPO na Soba yana cikin mutane hudu(4) da aka sanya a karar," in ji shi.

Dakta Nalado ya ce kararrakin bakwai din sun nemi kotu da ta umurci Sufeton ƴan sanda (IGP) da sauran su da aka hada a karar a dunkule da kuma daban-daban da su biya kowanne wanda suka kashe kuɗi Naira miliyan 200 (N200,000,000.00), wanda idan aka hada duka za su kai Naira biliyan 1.4.

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top