FALLASA: Badakalar Takardun Makaranta Da Za Ta Iya Cinye Kujerar Gwamnan Zamfara, Matawalle

MMS HAUSA
0

Daga Tanimu Salihu Mafara

Badaƙalar takardun makaranta na bogi da ake zargin gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle da shi yana da tada hankali, hujjojin kuma da suke yawo suna da ban mamaki. Wannan zancen ya wuce gaban yarfen siyasa, saboda hujjojin a bayyane suke kamar hasken rana.

Yana da matuƙar wahala a iya ɓoye gaskiya a wannan ƙarni namu, zamanin da ya zo da ci gaban fasahar da duk wani abu da ka ke nema zaka samu kafin ƙyaftawar ido. Idan mutum yana da wani abu da yake son ɓoyewa, zai baka tausayi, saboda komi a bayyane yake ga kowa.

Domin fahimtar irin gagarumar matsalar da Gwamna Matawalle ke ciki, akwai buƙatar a yi bayan ikan mutumin da ya cancanci zama gwamna da kuma aikin gwamna. 

Gwamna ya samo ikonsa ne daga kundin tsarin mulkin Nijeriya, kamar yadda yake a babi na ƁI, bangare na biyu, shafi na 176 cewa, “gwamna jiha shi ne shugaba a jiharsa”.

Gwamna shi ke jagorantar sashen gudanarwa, shi ne wuƙa da nama a duk wani abin da ya shafi gudanar da jihar. Gwamna ne ke tabbatar da doka, ya naɗa alƙalai a jiha da sauran naɗe-naɗe. A matsayin shugaba, dole ne gwamna ya zama ya siffantu da abubuwa bakwai: jajircewa, halin ƙwarai, bin ƙa’ida, yin komi a bayyane, faɗin gaskiya, bin diddigi da kuma ingantaccen shugabanci.

A halin da ake ciki, Gwamna Matawalle na fuskantar ƙalubale na yi masa kallon rashin gaskiya, saboda zancen takardun karatunsa na haifar da tarnaƙi, wanda abubuwan sun taru sun yi masa yawa, ga rashin iya mulki da rashin gogewa ga kuma batun gabatar da takardun boge. Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya samar da cewa duk wani wanda ke neman mulki dole ne ya samu shaidar kammala karatu aƙalla wacce ba ta gaza ta Sakandare ba. Dole ne ka je makaranta, ka samu ilimi zuwa matakin da za ka iya yin karatu, ka kuma yi rubutu don rattaba hannu kan muhimman takardu.

Tashin farko, inda za a ɓallo ruwa ga Gwamna Matawalle shi ne bin diddigin takardun makarantarsa, domin ganin cewa ya faɗi gaskiya ko a’a?

Gwamna Matawalle a zaɓukan shekarar 2015 da zaɓen 2019 ya gabatarwa da hukumar INEC takardar ‘technical’ wacce ma’aikatar ilimi shiyyar jihar Sakkwato ta ba shi a matsayin shaidar kammala koyon sana’ar hannu. A jikin takardar wacce aka ba shi a shekarar 1985 an rubuta cewa Bello Mohammed, wanda ke da lambar jarabawa 005, an haife shi ne a ranar 29 ga watan Fabrairun 1962.

A takardar kotu ta gyaran shekarar haihuwa wacce kawun Matawalle, Alhaji Bala S/Kaya Maradun ya cike, ya bayar da shaida cewa Bello Mohammed wanda aka Haifa a Maradun ta Jihar Zamfara, an haife shi ne a ranar 12 ga watan Fabrairun 1962. Wannan takardar gyaran shekarar ranar haihuwa an yi ta ne ranar 11 ga watan Mayun 2022 kuma tana ɗauke da sa hannu da tambarin babbar kotun jihar Zamfara.

Daɗin daɗawa, Gwamna Matawalle ya sake cike wata takardar a babbar kotun tarayya dake abuja, inda ya rantse cewa ingantaccen ranar haihuwarsa shi ne 12 ga watan Fabrairun 1962 ba 12 ga watan Fabrairun 1969 ba. Haka kuma a fasfo ɗin Matawalle na ƙasa da ƙasa (International Passport) mai lamba A50445292, wanda aka samar da shi a ranar 6 ga watan Yulin 2017, kuma ya daina aiki a ranar 5 ga watan Yulin 2022, ya nuna cewa an haifi Matawalle a ranar 12 ga watan Yulin 1962.

Inda gizo ke saƙar a nan shi ne a shaidar ranar haihuwar Gwamna Matawalle na jikin takardar shaidar kammala sakandare na satifiket ɗin NECO wanda kuma shi ne ya gabatarwa da hukumar zaɓe ta ƙasa ‘INEC’ a matsayin shaidar kammala karatun sakandare, cikin takardunsa na son yin takara a zaɓen 2023. A satifiket ɗin nasa na NECO, Bello Mohammed Matawalle mai lambar rajista 82806985CC ya zauna jarabawar NECO wacce aka yi a watan Yuni/Yuli ta shekarar 2018 a Universal Academy Kaduna, makaranta mai ɗauke da lamba 0140300. Wannan takardar ta NECO tana ɗauke da ranar haihuwar Gwamna Matawalle ne kamar haka: 28 ga watan Fabrairun 1979. Wanda idan aka duba, za a ga wannan ranar haihuwar ta jikin satifiket ɗinsa na NECO sam bai zo ɗaya da shaidar gyaran ranar haihuwar da ya yi guda biyu a kotu ba.

Babban abin damuwar a dukkan wannan matsala shi ne, ko dai Gwamna Matawalle bai zana wannan jarabawar NECO da kansa ba ko kuma sayanta ya yi da kuɗi. 

Domin kuwa jarabawar da yake iƙirarin ya zauna, wato ta watannin Yuni/Yuli NECO ‘Internal’, jarabawa ce da ɗaliban makaranta kaɗai ke zana wa. Wato dole ne ka faro daga SS1 zuwa SS3. Wannan tana da bambanci da NECO ‘External’ wacce ake rubutawa a watannin Nuwamba/Disamba.

Gwamna Matawalle a iƙirarinsa, wannan jarabawar NECO da ya zauna, kamar yadda muka bankaɗo, ya zauna ne tare da ‘ya’yansa Bello Aisha Matawalle, Bello Kausar Matawalle, Bello Yuhanasu Matawalle, da kuma Bello Zainab Matawalle duk a makarantar Universal Academy, Kaduna.

A shekarar 2000, irin wannan rashin gaskiyar ce ta janyo Salisu Buhari ya fashe da kuka a gaban ‘yan jarida, ya sanar da murabus ɗinsa a matsayin Kakakin Majalisar Tarayya, saboda an kama shi da laifin gabatar da takardun bogi. Salisu Buhari ya nemi afuwar ‘yan Nijeriya kan wannan rashin gaskiya da ya yi, ya kuma nemi a yafe masa.

A matsayina na mai kishin jiharmu ta Zamfara, bisa la’akari da irin hujjojin nan da suke a bayyane kamar hasken rana, zai fi mutunci ga Gwamna Matawalle ya mutumta kansa, ya mutumta ofishin gwamna, ya mutumta mutanen Jihar Zamfara ta hanyar bayyanawa duniya irin badaƙalar da yake ɓoyewa ta takardun makarantarsa. 

A baya dai, Salisu Buhari ne ya fi shahara da takardun bogi, amma daga yadda abubuwa ke tafiya, Gwamna Matawalle zai amshe wannan kambun daga hannunsa.

Doka ta yi tanadi kan wanda ya ke amfani da takardun bogi kuma yana sane, cewa duk wanda ya aikata haka, za a ɗaure shi a gidan kurkuku na tsawon shekara 14.

Tanimu Salihu Mafara shi ne Shugaban Kungiyar Zamfara Ina Mafita

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top