Asibitin MGK Ya Gabatar Da Sabon Tambarinsa Tare Da Karrama Wasu Ma'aikatansa

MMS HAUSA
0

A daren shekaranjiya Asabar 1 ga watan Oktoban 2022, daidai da ranar bikin 'yancin kan kasa, Asibitin MGK Healthcare dake Kano ya gabatar da taro domin godiya ga Allah bisa cikar Nijeriya shekaru 62 da samun 'yancin kai, shirya cin abinci, karrama wasu ma'aikatansa, tare da kuma mika jinjina ga wasu daga cikin masu hulda da asibitin. Da kuma gabatar da sabon tambarin asibitin a wani mataki na bunkasa ayyukan asibitin. 


Taron ya samu halartar 'yan'uwa da abokan arziki da masu hulda da asibitin, kuma ya gudana ne a harabar asibitin dake Plot 53 Road Karkasara, Gefen Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano daidai Sabuwar Kofar Fita, dake Jihar Kano.

A jawabinsa, wanda ya assasa kuma shugaban Asibitin, Malam Muhammad Garba ya ce makasudin shirya taron shi ne bayan murna da yi wa kasa addu'a bisa samun 'yancin kan Nijeriya shekaru 62 da suka gabata; "muna son amfani da wannan dama ma'aikata da muke tare da su a wannan asibitin namu, mu kara yaba musu bisa kokarin da suke nuna wa wajen jajircewa domin gabatar da ayyukan da ya doro a kawukanmu baki daya". 

Ya kara da cewa; "Sannan da sauran mutane da muke mu'amala tare da su; dukkannin Likitoci. Tunda babu wani waje da yake ginuwa da mutum daya. Haduwa ce kowa yana bada da ta shi gudummawa wajen ganin an taimaka wajen gabatar da ayyuka ga marasa lafiya da al'umma baki daya", ya lurantar.

Ya kuma ce; "mu taya junanmu murna domin karrama wasu daga cikinmu domin jajircewarsu sannan da kokarin ganin sauran sun kwafa daga irin wadannan abubuwan da suke gabatarwa. Duk mun taru ne wajen yi wa dan Adam hidima da bukatuwarsa. Tare da gode ma sauran mutanen da suke da yakini akanmu". 

Malam Muhammad Garba, har wala yau a wani bangare na jawabinsa, ya lurantar da cewa; "Harkar lafiya harka ce ta taimako da yake da bukatar gudummawa daga kowa da kowa". 

Ya kuma ce ba kishiyantar gwamnati suke ba, inda ya ce; "duk inda ka zagaya a duniya ba kawai gwamnati ce ke daukar harkar lafiya ba. A ko'ina ne a duniya, akan je wadansu wuraren lafiyar ne wadanda ba na gwamnati ba. Wadannan wurare ba suna zama kishiyoyi ga gwamnati bane, suna zama masu tallafawa ne", ya jaddada. 

Ya kara da cewa; "a yunkurinmu na inganta ayyukan lafiya na MGK, a kwanakin baya, mun yi wata yarjejeniya da mutanen Misra wanda muka sanya hannu akan fahimtar juna kan ilimi wajen gabatar da ayyukanmu a tare. Mun yi hakan, mun yarda za mu yi aiki a tare. Za su zo nan su ajiye mana daya daga cikin Likitocin su wanda zai kasance tare damu har zuwa wani lokaci. Ko da ya zama mutane sai sun je can, suna iya samun irin abin da za a musu a kasar waje a nan MGK. Tuni mun fara mu'amaloli tare da su, zai zama ya ci gaba da jagorantar sauran ma'aikata da muke tare da su", ya tabbatar. 

A na shi bayanin, Babban Jami’in gudanarwa na MGK Healthcare, Pharm. Isma’il Usman ya ce an kafa MGK Healthcare A 2016. Kuma an fara ne da bangaren sayar da magunguna kawai daga baya ya rika bunkasa shekara bayan shekara, wanda yanzu haka Asibitin ke aiki a tsawon awa 24 da bangarori birjik.

Ya kara da cewa sun gabatar da tiyata a bangarori da dama, domin suna da kwararrun likitoci da suke wannan aikin. Ya ce suna da manyan Likitoci a bangarori daban-daban da suka kulla alaka da su wanda suke gudanar da ayyukansu a asibitin wajen kula da kanana da manyan cututtuka, sannan suna da ingantattun kayayyakin zamani dake saukaka ayyukansu na inganta lafiyar al'umma. 

Pharm Isma'il ya ce suna da buri da fatan fadada Asibitin ta hanyar samar da wasu rassan Asibitin a fadin jihar Kano da Arewa da ma Nijeriya baki daya. "muna da tunanin a nan gaba MGK Healthcare za ta kai matakin da za mu rika samar da maganin da za mu rika aiki da shi a cikin asibitocinmu da wasu asibitoci a Nijeriya da ma duniya baki daya", Inji shi. 

Daga karshe an gabatar da sabon tambarin asibitin da za a rika amfani da shi wanda ya kasance ja da fari ne ga kafatanin mahalarta wannan taron.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top