Majalisar Matasan Arewa Ta Gargaɗi Gwamna Matawalle Kan Barazana Ga Shugabanta

MMS HAUSA
0

Majalisar Matasan Arewa 'Northern Youth Assembly' ta gargaɗi gwamna Matawalle bisa barazana ga rayuwar shugabanta reshen Jihar Zamfara.

Majalisar ta yi wannan gargaɗi ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Juma'ar makon da ya gabata a babban birnin tarayya Abuja.

Yayin gabatar da takardar manema labaran, mataimakin sakataren yaɗa labarai na Ƙungiyar ta ƙasa, Muhammad Hussaini Bauchi ya bayyana taron nasu a matsayin gargaɗi ga Gwamna Matawalle dangane da barazanar da yake yi ga Shugaban Majalisar Matasan Arewa reshen Jihar Zamfara, Kwamared Munnir Haidara Kaura.

Majalisar ta ce, ta yi mamakin irin abin da gwamnatin Zamfara ta aikata, wanda a maimakon ta zama mai bayar da tsaro ga rayukan al’umma sai  ta zama mai yin barazana ga rayuwa.

Sakataren yaɗa labaran ya ce: “muna son yin amfani da wannan dama wurin nuna rashin gamsuwarmu da irin abin da gwamnatin Jihar Zamfara ta aikata. Duk da Kwamared Munir Haidara Kaura ya rubuta takardar ƙorafi ga rundunar ‘yan sanda ta ƙasa reshen jihar Zamfara, Hukumar DSS da sauransu domin bayyana musu irin barazanar da gwamnatin Jihar Zamfara ke yi wa rayuwarsa. A namu ɓangaren, dole ne mu sanar da ‘yan Nijeriya yadda gwamnatin ta Zamfara ƙarƙashin jagorancin Bello Muhammad Matawalle take ci gaba da yin barazana ga rayuwar shugaban Majalisar Matasan Arewa reshen jihar ta Zamfara.

“Wannan abin Allah wadai ne da ƙyama ta kowacce fuska. A bisa haka ne muka shirya wannan taro na manema labarai, domin duniya ta sani cewa duk abin da ya samu Kwamared Munir Haidara Kaura, toh gwamnatin Zamfara da gwamna Matawalle ne abin tuhuma.” Inji shi
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top