Hukumar Kula Da Iyakokin Ruwan Kasar Nan Ta Bada Gudunmawar Kayayyakin Kula Da Lafiya

MMS HAUSA
0

Daga Bello Hamza

Hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan-NIMASA ta bada gudunmawar kayayyakin kula da lafiya a wasu asibitoci da ke yankin babban birnin tarayya, Abuja.

Wannan na kunshe ne a sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama'a na hukumar, Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai a birnin ikko.

Da yake gabatar da kayayyakin, Shugaban hukumar, Dr Bashir Yusuf Jamoh wanda Daraktan ayyuka na musamman a hukumar Mr Isichei Osamgbi ya wakilta, yayi bayanin cewa gudunmawar wata dama ce na kyautata dangantaka tsakanin hukumar da sauran hukumomin gwamnati da masu zaman kansu da kuma daidaikun jama'a.

Shugaban hukumar ya kara da cewa baya ga asibitin yankin Asokoro da ya amfana da wannan gudunmawa, ana sa ran sauran asibitocin da ke yankin na babban birnin tarayya su ma za su amfana.

Dr Bashir Jamoh har ila yau yayi nuni da cewa wannan gudunmawa na da nufin tallafawa kokarin gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki wajen inganta kiwon lafiya a fadin kasar nan.

Tunda farko a jawabin shi, babban sakatare a hukumar bada agajin gaggawa na birnin tarayya, kuma shugaban asibitin yankin Asokoro, Alhaji Abbas Idris ya bayyana godiyar shi ne ga hukumar ta NIMASA bisa wannan gudunmawar, yana mai nuni da cewa kayayyakin za su taimaka wajen inganta lafiya a yankin na babban birnin tarayya.

Kawo yanzu dai, hukumar NIMASA ta bada gudunmawar kula da lafiya, kayayyakin karatu, kayayyakin inganta tsaro da kuma kayayyakin rage radadi a jihohi daban-daban dake fadin kasar nan.

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top