Sarkin Kano, Aminu Bayero Ya Kai Ziyara Asibitin MGK Healthcare

MMS HAUSA
0


Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ziyarci Asibitin MGK Healthcare Services dake titin Karkasara dake karamar hukumar Tarauni a cikin garin Kano. Mai Martaba Sarkin ya ziyarci asibitin ne a yau Litinin 29 ga watan Agustan 2022.

Jim kadan da isarsa, tawagar MGK Healthcare Services a karkashin wanda ya assasa asibitin, Malam Muhammad Garba, da kuma Babban Daraktan Cibiyar lafiya ta Medica Overseas dake kasar Misra, Dr. Thamer Kazamel, wanda suka kulla yarjejeniyar fahimtar juna da Asibitin na MGK Healthcare, da sauran ma'aikatan asibitin sun yi wa Mai Martaba Sarkin Kano kyakkyawan tarba.

A cikin jawabinsa, wanda ya assasa asibitin, Malam Muhammad Garba, ya bayyana jindadinsa da godiyarsa bisa ziyarar da Mai Martaba Sarkin Kano ya kawo da kansa zuwa Asibitin; "wannan babban farin ciki ne a gare mu", inji shi. 

Ya kuma bayyana harkar lafiya a matsayin harka ta taimako. Inda ya ce a kokarinsu na fadada ayyukan asibitin ne ya sanya suka kulla alaka da likitocin na Misra. Sannan ya ce; "Muna sa ran alakar da muka kulla tare da wadannan likitoci na Misra zai zama abin alfahari, da ci gaba da taimakawa al'umma baki daya". 

Sannan ya nusasshe da cewa asibitin ya fara aiki fiye da shekaru bakwai da suka gabata, amma ya ce wannan rana ta musamman ce sakamakon ziyarar da Mai Martaba Sarkin Kano ya kawo musu. Sannan ya nusasshe da cewa; "mun samu nasarar kulla alaka da likitocin Misra wanda suka zo asibitin nan domin su zauna damu su gudanar da ayyukansu tare damu", ya jaddada. 

Shima a na shi jawabin, Dr. Thamer Kazamel, ya nuna jindadinsa bisa wannan ziyara da Mai Martaba Sarki ya kawo musu, inda ya ce; "na ji dadi sosai. Ba ni da kalmomin da zan iya bayyana farin cikina da kuma karamcinka. Za mu yi kokari wajen ganin mun yi aiki tukuru. Za mu yi amfani da fasaha a nan kusa wajen samar da tsarin kula da mara lafiya daga nesa, inda likita daga kasar waje zai duba mara lafiyar dake nan Nijeriya. Kuma lokaci bayan lokaci za mu rika kawo likitoci daga kasashen waje", ya tabbatar.


Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a na shi jawabin ya bayyana cewa kawo kwararrun likitoci daga kasar Misra da shugaban hukumar gudanarwa na Asibitin MGK Healthcare dake jihar Kano ya yi, babban ci gaba ne ga al'ummar Nijeriya masu fita zuwa kasashen wajen domin duba lafiyarsu.   

Mai Martaba Sarkin Kano, har wala yau ya yi wa bakin likitocin daga Misra barka da zuwa Kano, inda ya yi musu godiya da cewa; "muna godewa Ubangiji da ya nufa Allah ya kawo ku nan garin. Mungode da wannan kokari da kuka yi na zuwa nan."

Ya ci gaba da cewa: "muna fata zuwan na ku ya zama alheri ga kasarmu baki daya ba iya Kano ba. Muna kuma tabbatar muku da cewa nan gida ne a gareku. Muna fatan duk abin da za ku yi ku yarda cewa taimako za ku yi wa al'umma", ya nusasshe su.

A karshe Mai Martaba ya yi addu'ar Allah ya bada ikon bunkasa wajen a wasu wuraren ma tare da kawo ci gaba baki daya.

Bayan kammala jawabinsa, tawagar MGK Healthcare Services ta mikawa Mai Martaba Sarkin Kano kyauta ta musamman domin karrama shi.

Tunda farko, Sarkin da tawagarsa an zagaya da su sassa daban-daban na asibitin domin ganewa idonsa irin tsare-tsaren asibitin da kuma ingantattun kayayyakin aikin da aka tanada domin duba marasa lafiya. 

An zagaya da Sarkin da tawagarsa wuraren da ya hada da bangaren masu kula da ciwon hakori, bangaren bayar da magunguna, bangaren gwaje-gwajen cututtuka manya da kanana, bangaren da ke haska cututtukan dake jikin mutum, bangaren tiyata da ya hada da na kashi, karbar haihuwa, cututtuka, kwakwalwa da jijiya da kuma na zuciya, sannan da bangaren zirga-zirga da marasa lafiya da sauran su.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top