Babban mai faɗa a ji a Iraki, Moqtada al-Sadr ya yi ritaya daga siyasa

MMS HAUSA
0


Ɗaya daga cikin masu faɗa a ji a ƙasar Iraqi, wanda ya kasance a cikin rikicin da aka daɗe ana yi akan kafa gwamnati, ya ce ya yi ritaya daga siyasa.

Moqtada al-Sadr, babban malamin shi'a mai miliyoyin mabiya, ya sanar da matakin nasa ne a shafin Twiter.

Ɗaruruwan magoya bayansa sun yi sansani a wajen majalisar dokokin ƙasar har na tsawon makonni bayan sun yi tsinke har sau biyu tare da gudanar da zanga-zanga don nuna rashin amincewa da rikicin siyasar.

Dakarunsa sun yi fice wajen yaƙar sojojin Amurka bayan mamayar da suka yi a 2003.

Sanarwar ta Mista Sadr na zuwa ne kwanaki biyu bayan da ya buƙaci dukkan ɓangarori da kuma jiga-jigan da ke da hannu a harkokin siyasa su ajiye aiki sakamakon mamayar da Amurka ta yi wa Iraqi.

Jam'iyyarsa ta lashe mafi yawan kujeru a babban zaɓen da aka yi a Oktoban da ta gabata, amma daga baya ƴan majalisarsa sun yi murabus sakamakon rashin jituwa tsakanin su kan kafa gwamnati.

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top