Ɗan Takarar Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Ya Halarci Taron Masu Ruwa Da Tsaki Da Atiku

MMS HAUSA
0

Ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, Dr. Dauda Lawal ya halarci taron masu ruwa da tsaki na yankin Arewa maso Yamma.

Taron wanda aka gudanar yau Talata a dakin taro na Bristol dake Kano, ya samu halartar gabaɗaya 'yan takarar gwamna daga jihohi bakwai na yankin.

A yayin taron, wanda ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya yi don gudanar da tattaunawa ta musamman da ‘yan takarar gwamna na jihohin Arewa maso Yamma da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP daga yankin. Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasan kuma Wazirin Adamawa ya yi kira ga musamman ‘yan takarar gwamnan da su ci gaba da yin aiki don nasarar jam’iyyar.

Ya bayyana cewa, idan har PDP ta lashe zaɓen shugaban ƙasa wanda shi ne za a fara gudanarwa, toh babu makawa jam’iyyar za ta lashe sauran kujeru, kama daga na gwamna, sanata, da sauransu.

Da farkon fara taron dai an gabatar da mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na yankin Arewa maso Yamma, Alhaji Hayatu Gwarzo wanda ya yi maraba da baki tare da bayyana maƙasudin kiran wannan tattaunawa ta musamman. 

Bayan nan an gabatar da ‘yan takarar gwamna daga jihohi bakwai na wannan yankin. Dakta Dauda Lawal daga Jihar Zamfara, Ashiru Isa Kudan daga Jihae Kaduna, Mustapha Sule Lamido daga Jihar Jigawa, Sadiƙ Walid aga Jihar Kano, Janar Aminu Bande daga Jihar Kebbi, Sa’idu Umar daga Jihar Sakkwato.

Ɗan takarar gwamna na Jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan ne ya yi jawabi a madadin ‘yan uwansa ‘yan takara daga waɗannan jihohin Arewa maso Yamma guda bakwai. Ya bayyana jin daɗinsu ga irin wannan muhimmin taro, wanda a cewarsa ya ƙara kusanto ‘yan takarar da ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Cikin jiga-jigai da suka halarci wannan taro akwai gwamnan Jihar Delta kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a PDP, Ifeanyi Okowa, gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, shugaban jam’iyyar PDP ta ƙasa, Sanata Iyochia Ayu, tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo, tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema da dai sauransu.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top