Rahotanni daga gidan yarin Kuje mai matsakaicin tsaro da ke babban birnin Najeriya, Abuja na cewa an samu wata hatsaniya da ta kai ga rasa ran wani fursuna yau Litinin.
A cewar rahotannin, fursunan ya mutu ne bayan kasa ba shi kulawar lafiya da ta kamata.
Duk da cewa hukumomin gidan yarin sun tabbatar da mutuwar dan fursunan, amma sun ce an ba shi kulawa da ta kamata.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gidan yarin Chukwuedo Humphrey ya fitar, gidan yarin bata ce uffan ba kan hatsaniyar da aka samu.
-BBC Hausa