Rahotanni na cewa an sallami wasu matuƙa jirgin saman kamfain Air-France biyu sakamakon gwada ƙwanji da suka yi cikin jirgi.
Matuƙin jirgin da mataimakinsa sun ba hammata iska yayin da suke tuƙa jirgi ƙirar Airbus A320 daga Geneva zuwa Paris a watan Yuni kamar yadda jaridar Swiss News Outlet ta shaida.
Ma'aikatan jirgin sun shiga tsakani inda ɗaya daga cikin ma'aikatan ya tsaya tare da matuƙa jirgin har sai da jirgin ya sauka ba tare da matsala ba.
Faɗan nasu dai bai shafi sufurin jirgin ba, a cewar kamfanin jirgin.
Lamarin kuma ya faru ne bayan wallafa wani rahoto da hukumar da ke bincike kan sufurin jiragen sama ta Faransa ta yi ranar Talata da ya ce kamfanin jirgin yana sako-sako game da tsare-tsarensa na tsaro.