MGK Healthcare na farin ciki gayyatar al’umma don tunawa da Ranar Cutar Hanta ta Duniya ta 2022 wato ‘World Hepatitis Day 2022 Pop-Up’.
Wannan bayanin ya fito ne a wata sanarwa da Cibiyar lafiya ta MGK ta fitar a ranar Alhamis, inda ta sanar da cewa sannan za a yi wa al’umma gwajin cutar ta hanta ta ‘Hepatitis B’ kyauta da kuma wayar da kan jama'a akan cutar.
Shirin zai gudana ne a ranar 30 ga watan Yuli, 2022 a dakin tantancewa na Cibiyar da ke Plot 53 Road Karkasara, Gefen Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano daidai Sabuwar Kofar Fita, dake Jihar Kano.
Domin ƙarin bayani, a tuntuɓi wadannan lambobin; 09090900022 ko 09090909076, ko kuma 08067834890.
Haka nan zaka iya tuntuɓarmu ta hanyar adireshin Imel a info@mgkhealthcare.com ko mgkhealthcare@gmail.com ko ku ziyarci shafinmu na Intanet a www.mgkhealthcare.com