Jami'ar Maryam Abacha Ta Nada Mataimakin Shugaban Jami'ar FUDMA A Matsayin Memba A Majalisar Gudanarwarta

MMS HAUSA
0


Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, ta nada mataimakin shugaban Jami’ar Tarayya dake Dutsinma (FUDMA), Farfesa Armaya’u Bichi, a matsayin memba a majalisar gudanarwarta.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na FUDMA, Malam Habib Umar-Aminu ya fitar a ranar Asabar a Katsina.

Ya bayyana cewa nadin na Bichi ya biyo bayan taron kwamitin amintattu na MAAUN, wanda aka gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairu.

Shugaban Majalisar Gudanarwa kuma wanda ya kafa Jami'ar MAAUN, Farfesa Adamu Gwarzo, a lokacin da yake taya wanda aka nada murna, ya ce zabin nasa ya biyo bayan binciken kwakwaf da aka yi a tsakanin fitattun mutane dake da hazaka da jajircewa wajen bunkasa ilimi da ci gaban dan Adam. 

“Zabinka ya kasance saboda waɗannan halaye, musamman ma ƙwarewarka a fannin ilimi. Ka karɓi sakon taya murnata da gaisuwata,” mai magana da yawun ya ruwaito Gwarzo yana cewa.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top