Jami'ar MAAUN Kano Za Ta Kafa Cibiyar Bincike

MMS HAUSA
0

Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, za ta kafa cibiyar bincike a wani bangare na kokarin inganta Bincike da ci gaba.

Tuni dai wanda ya kafa Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya fara aiki domin samun tallafin bincike na kimanin dala miliyan 54.

Mataimakin Shugaba bangaren Gudanarwa/ Magatakardar MAAUN, Dakta Habib Awais Abubakar ne ya bayyana hakan a wani taron hadin gwiwa da wakilan Jami’ar Teknologi PETRONAS (UTP) da aka gudanar a dakin taro na MAAUN Kano a ranar Juma’a, 01 ga Yuli, 2022.

An kira taron ne domin tattaunawa kan yadda za a yi hadin gwiwa tsakanin MAAUN Kano da UTP.

Dakta Uwais ya ce kafa cibiyar binciken ya zama dole ta yadda za a inganta ci gaban bincike a jami’ar tare da samar da hadin guiwa a fannin bincike da sauran jami’o’in duniya.

“Duk da cewa MAAUN Kano tana da ‘yar'uwarta a Jamhuriyar Nijar da aka kafa kimanin shekaru tara da suka gabata, amma za a fi mayar da hankali a nan, domin muna son a ci gaba da martaba sunan jami’ar,” inji shi.

A nasa jawabin, shugaban MAAUN, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr, ya ce hadin gwiwar, idan ta kullu, za ta inganta musayar dalibai, da musayar tsangaya tare da inganta shirin karatun digiri na biyu da na uku. 


Ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin jami’o’i tare da yin kira ga wakilan UTP da su fito da fagagen da za a iya yin hadin gwiwa tsakanin UTP da MAAUN a taro na gaba wana aka tsara yi a ranar Litinin 4 ga watan Yulin 2022.

Tun da farko a jawabinsa, Dakta Zakariyya Uba Zango, ya ce jami’ar Teknologi PETRONAS da aka kafa shekaru 23 da suka gabata, tana gudanar da shirye-shirye a matakin digiri na farko da na gaba.

Ya bayyana cewa a halin yanzu, Jami'ar tana da dalibai sama da 6,000 wadanda suke karatun digiri na farko a yayin da dalibai 1,200
suke karatun digiri na biyu da kuma ɗalibai 1,200 wadanda suka yi rijista domin karatu 'Remedial'.

Dakta Zango ya kara da cewa kawo yanzu jami’ar ta samar da dalibai sama da 15,000 tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1997.

A cewarsa, UTP tana daya daga cikin mafi kyawun jami'o'i a Malaysia kuma tana a matsayi na 361 kuma tana ba da tallafin karatu ga masu digiri na farko da na gaba a yayin da ɗalibai ke zuwa jami'ar daga sassan duniya.

Dakta Zango, wanda ya dauki lokaci yana bayyana irin fa'idar da hadin gwiwar za ta bayar a lokacin da aka sanya hannu, ya ce Jami'ar tana da Cibiyar bincike da ci gaba wanda ke daukar nauyin masu bincike, ya kara da cewa UTP tun a shekarar 2010 ta samu tallafin da ya kai miliyan 588 na ringgit na Malaysia.

Taron ya samu halartar Injiniya Bashir Garba wanda ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin jami'o'i a fadin duniya.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top