Dakta Dauda Lawal Ya Yi Jawabi A Taron Masana Tattalin Arziki Na Duniya A Birtaniya

MMS HAUSA
0

Daga Bello Hamza

A ranar Alhamis 30 ga Yulin 2022 ne dan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal ya gabatar da jawabi a wani babban taron masana tattalin arziki na duniya a yankin Glasgow da ke Birtaniya.

Dauda Lawal wanda shi ne ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara a ƙarkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, kuma tsohon babban daraktan First Bank ya amshi lambar girmamawa tare da gabatar da jawabi ne a taron masana mai taken ‘The 2022 Reputable Banks and Fintech Awards/Conference (RBFA)’.

Baya ga mashahuren masana tattalin arziki da suka halarci taron daga sassan duniya, manyan bankuna, kamfanonin inshora, da masu zuba hannun jari duk sun halarta.

Masu fashin baƙi kan harkokin yau da kullum sun ambaci taron na wannan shekara a matsayin ɗaya daga cikin wadanda suka fi armashi a tsawon shekarun da aka kwashe ana gabatarwa.

Yayin da yake gabatar da jawabinsa, Dauda Lawal ya maida hankali wurin jawo hankalin masana tattalin arziki da su waiwaiyi Afirka da irin tarin albarkatun da take da su, musamman ma Nijeriya. 

A cewarsa, lamari ne da ke buƙatar masu zuba hannun jari su shigo domin raya tattalin ƙasashen Afirka. 

A ƙarshe an gabatar da kambun shaidar girmamawa ga Dakta Dauda Lawal, a matsayin sanannen masanin tattalin arzikin da ke bada gudummawa ga wannan fanni a fadin duniya.

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top