2023: INEC ta fitar da sunan Sadiq Wali a matsayin ɗan takarar gwamna na jam'iyar PDP a Kano

MMS HAUSA
0


A ranar Juma’a ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana sunan Sadiq Aminu-Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa, jam’iyyar PDP ta jihar ta rabu gida biyu, inda ko wanne bangare ya gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda ya haifar da Mista Wali da Muhammad Sani-Abacha dan marigayi shugaban mulkin soja a matsayin ‘yan takarar gwamna.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bangaren Shehu Sagagi da ya gabatar da Mista Sani-Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar.

Sai dai a wani yanayi na daban, ofishin na INEC na Kano a yau Juma’a sai ya fitar da sunan Wali tare da abokin takararsa, Yusuf Dambatta a matsayin ‘yan takarar gwamna da mataimakinsa a zaben 2023.

Abba Kabir-Yusuf, wanda ke daga tutar jam’iyyar , NNPP, shi ma ya shiga jerin sunayen tare da abokin takararsa, Aminu Abdulsalam.

Haka shima ɗan takarar gwamna a jam'iyar PRP, Salihu Tanko Yakasai, sunansa ya fito.

Sannan Sheikh Ibrahim Khalil, ɗan takarar gwamna a jam'iyar ADC, yana cikin jerin sunayen.

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top