Mai Martaba Sarkin
Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya inganta masallacin Maryam Abacha American
University ta Nijeriya dake Kano zuwa matsayin masallacin Juma’a.
Sarkin ya sanar
da inganta masallacin ne a lokacin da kwamitin masallacin karkashin jagorancin
shugaban MAAUN, Farfesa Mohammad Israr ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa
a ranar Talata.
Bayero wanda ya
yi magana ta bakin Wazirin Kano, Alhaji Sa’ad Muhammad, ya ce inganta
masallacin daga masallacin koyaushe zuwa masallacin Juma’a zai ba dalibai damar
gudanar da sallar Juma’a ba tare da yin tattaki zuwa wurare masu nisa don
halartar sallar ba.
Ya kuma bukaci
mahukuntan Jami’ar da su tabbatar da bin duk ka’idojin da suka shafi kafa
masallacin Juma’a kamar yadda Shari’a ta tanada.
Sarkin ya yabawa
wanda ya assasa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa gina masallacin.
Majalisar Limaman
Masallatan Juma’a na jihar ta kuma amince da matakin da Sarkin ya dauka na
daukaka masallacin zuwa matsayin masallacin Juma’a.
Tun da farko a
nasa jawabin, Hakimin Kawo Alhaji Kabiru Garba wanda ya jagoranci kwamitin
masallacin zuwa fadar, ya ce masallacin ya cancanci wannan karramawa domin Jami’ar
ta bi tsarin da ya dace na kafa masallacin Juma’a ta fuskar nesa da masallaci zuwa
sauran masallatan Juma'a dake yankin da kuma kayan aiki da ake bukatar a sanya
su.
Basaraken ya ce
masallacin ya cika dukkan sharrudan da ake bukata na kafa masallacin Juma’a,
sannan ya gode wa Sarkin bisa yadda ya amince da inganta masallacin, ya kuma
bukaci mazauna yankin da su yi amfani da wannan wuri sosai.
Idan dai za a
iya tunawa, a kwanakin baya ne wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Abubakar Gwarzo
ya gabatar da takardar nadi ga Babban Limamin Jami’ar, Sheikh Muhammad Hassan.
Kafin a nada shi
Babban Limamin Masallacin Juma'a na MAAUN, Sheikh Hassan ya kasance Limami a
gidan Marigayi Janar Sani Abacha da ke kan titin Gidado, Nassarawa GRA, Kano.