Jami'ar MAAUN Za Ta Kashe Naira Miliyan 500 Wajen Horas Da Dalibanta Kan Kere-kere

MMS HAUSA
0

UNESCO-REF ta horas da daliban Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), dake Kano kan muhimmancin shirin TAP (The August Project) a ranar Alhamis, 23 ga Yuni, 2022.

Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) za ta kashe Naira miliyan 500 domin horar da dalibanta na MAAUN Kano da kuma MAAUN Maradi a Jamhuriyar Nijar kan fasahar kere-kere.

Manufar horon ita ce bai wa ɗalibai ilimi kan yadda za su ci gabantar da kansu ko da bayan kammala karatun.

Wanda ya assasa MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bayyana haka ne a wata lacca da aka shirya wa daliban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya da ke Kano, wadda UNESCO ‘Read and Earn Federation’ (UNESCO-REF) ta shirya.

Ya ce akwai bukatar a horas da daliban ta yadda za su rika yin kirkire-kirkire da kuma ba su ilimin yadda za su nemo hanyoyin magance dimbin kalubalen rayuwa da ke fuskantar matasa a kasar nan.

"Za mu yi amfani da kudi wajen bai wa daliban ilimi saboda mutane na da bukatar samar da mafita, suna da bukatar kuma zurfafa tunani kuma su kasance masu kirkire-kirkire tare da fito da hangen nesa," in ji Farfesa Gwarzo.

Wanda ya kafa Jami’ar, ya bayyana shirinsa na tallafa wa daliban da suke da hangen nesa domin tabbatar da burinsu, ya ce jami’ar za ta yi aiki a kan ayyukan.

A jawabinsa na maraba, Shugaban MAAUN, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr ya yaba wa Shugaban Hukumar UNESCO-REF, Yarima Abdulsalami Ladigbolu kan yadda ya dauki wannan mataki domin karantar da dalibai a kan shirye-shiryen UNESCO-REF. 

Ya ce shirin zai bai wa daliban damar fahimtar bukatar duniya da nufin kulla alaka domin ci gaban kansu a rayuwarsu.

Tun da farko da yake gabatar da jawabinsa, Shugaban Hukumar UNESCO-REF, Yarima Abdulsalami Ladigbolu ya ce an gudanar da laccar ne domin fadakar da daliban muhimmancin aikin UNESCO-REF TAP wanda aka tsara shi domin bunkasa hazikan cikin gida da nufin bai wa matasa dama su zama masu amfani a duniya kuma su ƙara wa takardunsu ƙima.

Ladigbolu, wanda ya dauki lokaci yana bayyana muhimmancin ayyukan TAP, ya ce shirin, na tsawon makonni shida, yana kan intanet, kuma zai ba wa daliban damar samun hanyar sadarwa ta duniya domin kulla alaka da abokan hulɗa a fadin duniya domin ci gaban kansu.

A cewarsa, daliban da suka kammala ayyukan na TAP suna da damar amfanuwa da shirin sosai musamman a bangare hudu na shirin wanda suka hada da nagartaccen jagoranci da kuma bunkasa tattalin arziki tare da tattalin arziki na zamani.

“Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya ita ce jami'a daya tilo da ta shiga wannan shirin saboda manufar MAAUN ya wuce Nijeriya da Afirka ma baki daya.”

Bayan laccar, an kaddamar da tutar shirin UNESCO-REF TAP a matsayin wani bangare na ayyukan tsara sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin abokan huldar biyu.

Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top