Za6en 2023: Atiku Ya Yi Alkawarin Sake Fasalin Nijeriya

MMS HAUSA
0


Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana shirinsa na sake fasalin Nijeriya domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da tsaro, idan har aka zaɓe shi a matsayin shugaban kasa.

Atiku, wanda ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da wakilan zaɓe na jam’iyyar PDP a jiya Lahadi a Abia, ya ce zai kawo sauyi a ƙasar idan aka ba shi dama.

Ya ce in dai ƴan ƙasa suna so su cimma muradun su, akwai bukatar jam’iyyar PDP ta samu nasara a zaben 2023.

Ɗan takarar ya ce takardarsa ta mayar da hankali ne kan muhimman abubuwa guda biyar da su ka haɗa da haɗin kan ƙasa, bunƙasa tattalin arziki, tsaron ƙasa, ilimi da kuma sake fasalin ƙasa.

"Tare za mu iya cimma dukkan waɗannan manufofin idan muka hada kai a jam'iyya," in ji shi.

Har ila yau, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Abia, Cif Asiforo Okere, ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki sun ji dadin karbar ɗan takarar shugaban ƙasar.

Okere ya ce irin gudunmawar da ɗan takarar shugaban ƙasa ya bayar ga jam’iyyar ba za ta taɓa yin kasa a gwiwa ba.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya yi wa Atiku jagora ya kuma biya masa bukatunsa na zama shugaban kasar Najeriya.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top