Shugabar Kwamitin Amintattu na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, Hajiya Dr Maryam Sani Abacha ta bukaci mahukumtan jami’ar da su nada Sheikh Muhammad Hassan a matsayin babban limamin masallacin Juma’a na jami’ar.
Sheikh Hassan shi ne Limamin gidan Marigayi Janar Sani Abacha dake kan titin Gidado, Nassarawa GRA, Kano.
Bukatar nadin Sheikh Hassan a matsayin Babban Limamin Masallacin Juma’a na MAAUN na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan Talata 3 ga watan Mayu, 2022, mai dauke da sa hannun Maryam Abacha, kuma aka rabawa manema labarai a Abuja a ranar Laraba.
Dakta Maryam Abacha ta bayyana cewa a cikin wasikar, bukatar ta ta taso ne bisa hujjar cewa Sheikh Hassan yana da ilimin addinin Musulunci da ake da bukata da kuma cancantar gudanar da Sallah a Masallacin duba da kasancewarsa mai haddar Al-Qur'ani kuma amintacce.
A cewarta, Sheikh Hassan yana da ilimin da ake bukata a fannin Fikihu, Shari'a da kuma iya harshen Larabci.
“a don haka muna so mu tabbatar wa duniya cewa Sheikh Muhammad Hassan shi ne babban limamin masallacin Juma’a na MAAUN Kano, muna taya shi murna da farin ciki tare da yi masa fatan shiriyar Allah,” in ji Maryam Abacha a cikin wasikar.
An haifi Sheikh Hassan a garin Gamborin Gala da ke jihar Borno a shekarar 1966. Ya kammala karatun kur'ani a shekarar 1972, ya kuma kammala haddar Alkur'ani a shekarar 1985.
Hakazalika a shekarar 1991 ya sake rubuta kur'ani mai tsarki da hannunsa sannan a shekarar 2018 ya halarci taron manyan limamai na masallatan Juma'a a kasar Morocco.