Sabon shugaban Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), dake Kano, Farfesa Mohammad Israr daga Indiya, ya fara aiki a ranar Litinin.
Da yake magana a yayin da yake mika ragamar shugabancin Jami'ar, Mukaddashin shugaban Jami'ar, Farfesa Mohammed Sanusi Magaji Rano ya ce akalla sabbin dalibai 715 ne aka bai wa gurbin shiga Jami'ar kuma suka yi rijista ya zuwa yanzu.
Ya mika godiyarsa ga shugaba kuma wanda ya kafa Jami'ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa ba shi damar rike wannan mukamin na wadannan lokuta.
Har wala yau ya kuma sake mika sakon jinjina ga Farfesa Gwarzo bisa yarda da amanar da ya sake dora masa kari kan wadanda ya yi a baya, inda ya nada shi a matsayin sabon Sakataren Kungiyar Jami'o'i masu zaman kansu na Afrika (APPU).
Tunda fari, a yayin jawabin gabatarwa, wanda ya kafa Jami'ar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya ce an shirya taron ne domin mika ragamar shugabancin Jami'ar ga sabon shugaba, Farfesa Mohammad Israr wanda ya zo daga Indiya.
Ya jinjinawa Kwamitin kula na membobi Bakwai a karkashin shugabancin Dr. Nura A. Yaro bisa sadaukarwa da jajircewa da suka nuna tare da gudummawar da suka bayar wajen ganin Jami'ar ta fara aiki cikin nasara.
Ya ce duk da Kwamitin ya kammala aikinsa, amma Kwamitin zai ci gaba da bayar da shawarwarin da yakamata ga sabon Shugaban Jami'ar a yayin da bukatar hakan ta taso.
A na shi bayanin, Shugaban Kwamitin, Dr. Nura Yaro ya ce Kwamitin wanda aka kaddamar da shi a ranar 11 ga watan Janairun 2022 domin tabbatar da Jami'ar ta soma aiki ya yi nasarar rijistar dalibai 715.
Ya lurantar da cewa Kwamitin ya samu wannan nasarar ce da aka yi zato daga gare su sakamakon cikakkiyar goyon baya da hadin kai ba tare da katsalandan ba da suka samu daga wanda ya kafa Jami'ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo.
Kazalika, a na shi jawabin, sabon Shugaban Jami'ar, Farfesa Mohammad Israr ya yabawa Farfesa Gwarzo bisa ba shi wannan aiki da ya yi, tare da alkawarin ganin ya yi aiki tukuru wajen tabbatar da cewa Jami'ar MAAUN ta kasance daya daga cikin mafi inganci a tsarin Jami'o'i mafi inganci na duniya.
Bayan taron mika ragamar shugabancin Jami'ar, an zagaya da sabon shugaban wurare daban-daban da ya hada da Masallacin Juma'ar Jami'ar, dakunan kwana na musamman da kuma dakunan dalibai da sauran su.