Muddin PDP Na Son Amsar Ragamar Mulkin Nijeriya Cikin Ruwan Sanyi Ta Bai Wa Tambuwal Tikiti, TCO Ga Delegates

MMS HAUSA
0


Kwamitin yakin neman zaben Tambuwal (TCO) ya bukaci Daliget na jam'iyyar PDP da su yi zurfin nazari tare da amincewa wajen bai wa Alhaji Aminu Waziri Tambuwal kuri'unsu domin ya samu zarafin zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar da nufin tunkarar matsalolin da suka yi wa Nijeriya dabaibayi.

Shugaban kungiyar yakin neman zaben (TCO), Prince Daniel, shine ya shaida hakan ta cikin sanarwar da ya raba wa 'yan jarida, ya mai cewa lokaci ya yi da za a hada karfi da karfe domin ceto Nijeriya daga halin da take ciki a yanzu tare da zabin nagartaccen da zai iya kwato mulki daga hannun APC.

Ya ce, yanzu kan kowa ya waye, an san masu son ci gaba da kuma masu mayar da lamura baya, ya ce, ba sabon labari ba ne yadda abubuwa suka cakude a kasar nan, wanda ake bukatar jajirtaccen shugaban da zai fuskancesu a karkashin tutar jam'iyyar PDP, domin ya yi mata takarar shugaban kasa.

Daniel yake cewa: "In dai maganar jajirtaccen mutum ake wanda zai tserar da Nijeriya daga halin kuncin da take ciki, to ba a bukatar wani dogon nazari, domin kuwa Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ne kadai zai iya wannan namijin aikin. Domin kuwa kowa ya shaida irin kalubalen da ake fuskanta a kasar nan. 

"Saboda haka akwai bukatar a fara bayyana jajirtattu irinsu. Kuma hanyoyin maganta matsalolinmu a bayyane suke, inda mafi yawansu ma suna nan rubuce cikin ma'aikatu da dama na gwamnatoci. An gaza aiwatar da su ne saboda saboda gazawar shugabanci."

Ya kara da cewa, "Duk da wannan tarin kalubalen, jam'iyyar PDP ta yi rashin nasara a zabukan shugaban kasa guda biyu da suka wuce a tsahon shekaru bakwai da suka gabata, yanzu kuwa dama ta samu da za a zabi nagartaccen dan takara da zai iya fuskantar jam'iyya mai mulki har ma a samu nasara, wanda Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ne kadai zai iya yin wannan namijin kokarin."

Ya bayyana dalilansu na son Tambuwal ya zama Shugaban Kasa, "Idan ka dauke kasancewar Tambuwal na matsayin kwararren lauya, jajirtaccen mai hidimtawa al'umma, haka nan kuma masanin bangarorin gwamnati na zartarwa da majalisa. Ya kasance mutum mai nagarta da kyawawan halaye sama da zango biyu da yayi a harkokin siyasa. Yanzu da kawunan 'yan Nijeriya suka rarraba fiye da ko yaushe, jam'iyyar PDP na bukatar dan takarar da zai zama karbabbe a kowanne yanki na kasar nan, wanda ya zaga kowanne loko da sako a zamansa na tsohon kakakin majalisar wakilai ta ƙasa. Shi ne zai iya daukar kowanne nauyi na kasar nan kamar yadda ya dauki nauyin dukkanin ayyukan majalisa ta 7.

"A bangaren tsaro kuwa, zai iya fuskantar kowanne kalubale, kamar yadda ya yaki na jihar, inda ya saka hannu akan dokar kalubalen tsaro, tare da samar da motoci 500, babura 765, gidaje 132 ga jami'an tsaro na kasa, ban da man zubawa a ababen hawan da kuma alawus dinsu.
Saboda haka ya fahimci matsalar tsaron kasar nan kuma zai yi aiki da masu ruwa da tsaki a lamarin da samar da kayan aiki, domin a yaki abin a fadin kasa gaba É—aya."

"Yajin aiki malaman jami'a ya zamo ruwan dare, inda malaman kwalejoji ke shirin bin bayansu. Inda gwamnatin tarayya ta yi biris da harkokin ilmi wanda ya zamo kashin bayan kowanne abu."

"Saboda haka da zarar ya dare shugabancin kasar nan zai kawar da wannan, domin kuwa yanzu haka yana ware kaso 29% ga bangaren ilmi a kasafin kudin jihar Sokoto. Dukkanin wasu kalubale da ake fuskanta a kasar nan, ana bukatar jajirtaccen shugaba wanda ba zai dinga shugabantar kasar daga asibiti ba, wanda Tambuwal yana da kosashshiyar lafiya, kuma bai tsufa ba, domin shekarunsa 56 ne kacal," a cewar kungiyar.

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top