Ma’aikatar kudi ta Najeriya ta musanta zargin cewa Babban Akantan kasar ya ambaci sunan ministar kudi a zargin da ake masa na halasta kudaden haram da karkatar da kudaden al’umma.
A makon jiya ne hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama Akanta Janar din bisa zarginsa da almundahana ta naira biliyan 80.
Ofishin ministar kudi da tsare-tsaren kasa Zainab Shamsuna Ahmed, sun wallafa a shafinsu na Facebook inda suke musanta zargin cewa babban akantan Najeriya Ahmed Idris, ya shafa wa ministar kashin kaji a zargin da ake masa na almundahanar da ta kai naira biliyan damanin.
Ma’aikatar kudin ta ce an ja hankalinsu game da wani labarin da ta ce na karya ne da aka yada a shafukan sada zumunta, wanda ke cewa babban akantan kasar ya shaidawa wadanda suke masa tambayoyi cewa ministar kudin ta mallaki kadarori a biranen Abuja da Kaduna da kuma Dubai da sunan mijinta.
Sanarwar ta yi kira ga jama'a da su yi watsi da labarin saboda acewarsu babu wani zargi da aka yi mata makamancin wannan.
A ranar Litinin 16 ga watan nan ne, hukumar EFCC da ke yaki da hanci da rashawa ta sanar a shafinta na Facebook cewa ta kama babban akantan bisa zarginsa da karkatar da kudade.
Ta ce ya yi hakan ne ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi, wadanda suka kai naira biliyan tamanin, al’amarin da yasa ma’aikatar kudi ta Najeriya, dakatar da Ahmad Idris.
A karshen mako ne kuma, gwamnatin Najeriya ta sanar da nada Anamekwe Nwabuoku a matsayin mukaddashin babban akanta Najeriya.