Wakilin
almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a Zariya wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a,
Shaikh Abdulhamid Bello a hirar da ya yi da manema labarai a Zariya ciki harda
wakilin Jaridar MAFITA jim kadan da kammala sallar Idi ta bana a ranar
Litinin 2 ga watan Mayun 2022 a makarantarsu ta Fudiyya dake Babban Dodo Zariya,
Shehin Malamin ya yi karin haske dangane da abin da ya faru a ranar Kudus a
Zariya.
Shehin Malamin ya fara
da cewa; “Taron tunawa da ranar Qudus wani taro ne na shekara-shekara wanda
musulmin duniya da masu hankali ke nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da
suke cikin mawuyacin hali a kowacce rana a hannun Sahayoniyawan Haramtacciyar kasar
Isra'ila. A bana an gudanar da muzaharorin ne a kusan dukkanin manyan biranen
duniya. A Nijeriya an gudanar da muzaharorin ne na lumana a garuruwa sama da
hamsin. Babu inda aka kai wa muzaharar hari sai a Kaduna da Zariya wanda ya yi
sanadin shahadar mutum daya a Kaduna tare da raunata dimbin ‘yan uwa musulmi maza
da mata da harsashi mai rai da jami’an tsaron Nijeriya suka yi. Hakazalika an
kama mutane da dama da suka hada da mata da kananan yara, da dama daga cikinsu
da raunukan da ke barazana ga rayuwarsu sakamakon harbin da ‘yan sanda suka yi
tare da garkame su a hannun ‘yan sanda ba tare da samun kulawar likitoci ba”,
ya labarta.
Har wala yau Shehin
Malamin ya ce; “muzaharar ta bana a Zariya sun kai mata hari ne bisa makircin cewa
muzaharar ta kona ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari da wata mota. A tarihin yake
cewa an kwashe sama da shekaru arba’in (40) ana gudanar da muzaharorin ranar
Kudus a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky inda a
kodayaushe ake tashi lafiya lau har sai dai idan jami’an tsaro ne suka zo suka kawo
wa masu muzaharar hari. A don haka abin takaici ne yadda bayan kai harin ga
‘yan kasar da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda suke amfani da ‘yancinsu na
gudanar da muzaharar lumana, amma kuma har ‘yan sandan za su iya ci gaba da
tuhumar masu muzaharar da laifin da wasu ‘yan iska da aka dora wa alhakin tayar
da hargitsi suka aikata domin a kama su da laifi tare da tabbatar da kuma
tabbatar da munanan laifukan da suka aikata”, ya lurantar.
Shaikh Abdulhamid Bello
ya ce; idan dai za a iya tunawa, kimanin watanni ashirin da suka gabata a
Kaduna a yayin gudanar da tarukan tunawa da Ashura an dauki jami’an ‘yan sanda a
kyamara suna cinna wa motar su wuta, inda ya ce; “wannan wani hali ne da ‘yan
sandan Nijeriya suka kware a kai suke kuma yi domin tabbatar da zaluncin da
suke yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Me ya sa jami’an tsaron
Nijeriya ba za su karkatar da duk karfinsu da dukiyarsu wajen yakar ‘yan fashin
daji da sauran miyagun da suka addabi zaman lafiyar Al’umma ba”, ya tambaya.
Da ya waiwayo kan batun
ranar Kudus kuwa, Shehin Malamin ya ce; “Batun ranar Qudus ta duniya ta goyon
bayan ‘yan uwanmu Palastinu lamari ne na imani da mutuntaka. A maimakon zama
namun daji da nuna rashin wayewa ta hanyar kai hari ga mutanen da ba su ji ba
ba su gani ba, me ya sa gwamnatin Nijeriya ba za ta shirya irin na ta
muzaharorin ba na nuna goyon baya ga haramtacciyar kasar Isra'ila da Sahayoniyawan
da suka yi kwacen kasar da ba na su ba suke zubar da jinin al'ummar Palastinu
da ake zalunta?
“Muna so mu bayyana tare
da jaddada cewa ba mu da hannu a cikin kona mota da kuma makircin karya da suke
yadawa na kona ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari. A don haka muna kira da a
gaggauta sakin duk wanda ke hannun ‘yan sanda. Hakazalika muna son mu yi amfani
da wannan dama wajen yin kira ga gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta sakin
takardun fita na Shaikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenat domin ba su damar
kula da yanayin da suke ciki na rashin lafiya”, ya karkare.