Farfesa Gwarzo Ya Mika Wa Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Jami'ar MAAUN Kano Takardar Soma Aiki

MMS HAUSA
0


Wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), Kano, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya gabatar da takardar nadi ga Babban Limamin Jami’ar, Sheikh Muhammad Hassan.

Kafin a nada shi Babban Limamin Masallacin Juma'a na MAAUN, Sheikh Hassan ya kasance Limami a gidan Marigayi Janar Sani Abacha da ke kan titin Gidado, Nassarawa GRA dake Kano.

Da yake mika wa Sheikh Hassan wasikar, wanda ya kafa ta ya ce nadin ya zo ne bisa bukatar shugabar kwamitin amintattu na Jami’ar, Hajiya Maryam Sani Abacha.

 “Babu wani abu da mahaifiyarmu Hajiya Maryam Abacha za ta nema a wurinmu da ba za ta samu ba, shi ya sa muka yanke shawarar barin namu muka nada Sheikh Hassan.

A cewarsa, Sheikh Hassan yana da ilimin addinin musulunci da ake da bukata domin gudanar da sallah a masallacin.

A don haka ya bukaci wanda aka nada da ya guji duk wani abu da zai iya inganta kowace kungiya a yayin gudanar da aikinsa na babban limamin masallacin.

“Ba mu sa ran za ku tallata siyasa ko wata kungiya ba, kasancewar daliban Jami’ar sun fito ne daga dukkannin bangarorin addini.

“A don haka, kofofinmu a koyaushe a bude suke ga duk wata shawara mai ma’ana don ci gaban Jami’ar da inganta zaman lafiya a cikin jami’ar,” inji shi.

A nasa jawabin, Sheikh Hassan ya godewa wanda ya kafa kuma shugaban hukumar gudanarwa ta jami’ar, Farfesa Abubakar Gwarzo bisa wannan nadin.

Ya yi alkawarin gudanar da aikinsa kamar yadda Shari’a ta tanada domin a cewarsa nadin amana ce kuma zai yi bayanin ayyukansa a lahira.

An haifi Sheikh Hassan a garin Gamborin Gala da ke jihar Borno a shekarar 1966. Ya kamalla karatun kur'ani a shekarar 1972, ya kuma kammala haddar Alkur'ani a shekarar 1985.

Hakazalika a shekarar 1991 ya sake rubuta Kur'ani mai tsarki da hannunsa sannan a shekarar 2018 ya halarci taron manyan limamai na masallatan Juma'a a kasar Morocco.

Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top