Gloria Nneka 'yar uwar Matthew da Linus Audu, sojojin nan biyu da aka kashe a wani kwanton ɓauna da aka yi musu a jihar Imo mako biyu da suka wuce, ta bayyana yadda ta ji da samun labarin kashe ma'auratan da aka yi.
Wasu ƴan bindiga ne suka kashe Linus Audu, wani tsohon jami'in soja da matarsa Private Gloria Matthew tare da datse musu kawuna a jihar Imo a ranar Asabar 30 ga watan Afrilun 2022.
Shi ma ɗan'uwan Linus ya shaida BBC Igbo cewa an sace ƙanin nasa tare da binne shi a wani rami.