Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sadu da iyalan da suka rasa rayukansu sakamakon fashewar da aka samu a Kano a makon da ya gabata.
Shugaban wanda ya je Kano domin ƙaddamar da bikin makon rundunar sojin sama ta Najeriya inda rundunar ke cika shekara 58 da kafuwa.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa shugaban ya jajanta wa iyalan mutanen da wannan hatsari ya rutsa da su da Sarkin Kano da kuma gwamna kan wannan lamari.