Ƴan Nijeriya Sun Kashe Sama Da Naira Biliyan 100 Kan Neman Ilimi A Ƙasashen Waje Cikin Wata Uku

MMS HAUSA
0

Wata ƙididdiga daga Babban Bankin Najeriya wato CBN ta nuna cewa ƴan Najeriya sun kashe aƙalla dala miliyan 220.86 kan karatu a ƙasar waje daga Disambar 2021 zuwa Fabrairun 2022.

Hakan na nufin sun kashe sama da naira biliyan 100 a kuɗin Najeriya.

Jaridar Punch a ƙasar ta ruwaito cewa CBN bai bayyana adadin da yan ƙasar suka kashe a watan Maris da Afrilu da Mayu ba, inda bankin ya ce akwai yiwuwar adadin da ya fitar na daga Disambar 2021 zuwa Janairun 2022 a samu sauyi.

Ɓangaren ilimi musamman na jami'o'i a Najeriya na cikin wani hali sakamakon irin yajin aikin da malaman jami'o'i ke yi.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top