Ƴan IPOB Sun Ƙone Sakatariyar Ƙaramar Hukuma A Anambra

MMS HAUSA
0


Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta tabbatar da ƙona shalkwatar Ƙaramar Hukumar Idemili ta Arewa da ke Ogidi a jihar Anambra a safiyar yau Litinin.

DSP Tochukwu Ikenga, jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar , ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ya yi da NAN ta wayar tarho a yau a Awka.

Ya ce maharan, waɗanda da ake zargin mambobin haramtacciyar ƙungiyar IPOB ne, sun kai harin kan shelkwatar Ƙaramar Hukumar da misalin karfe 2 na dsrr- yau.

Ikenga ya ƙara da cewa haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro da mutanen gari ne ya sanya a ka samu nasarar fatattakar ƴan ta’addan.

“Yayin da mu ke magana, har yanzu jami’an tsaro na nan kan lamarin, kuma muna tsare wajen.

"Dole ne in kara da cewa al'ummar gari sun taka rawar gani wajen fatattakar ƴan ta'addan nan, wasu da ga cikin su ka tare da jami'an tsaron su ka fafata da ƴan ta'addan,"
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top