Tsokaci A Kan Sabon Shugaban NPA, Mohammed Bello-Koko

MMS HAUSA
0

Daga Bello Hamza, Abuja

A ranar 15 ga watan Fabrairu 2022 ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mohammed Bello-Koko a matsayin sabon shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA), Daraktan watsa labarai na ma’aikatar Sufuri, Eric Ojiekwe ya bayar da sanarwa nadin a takardar manema labarai da aka raba a Abuja, ya kuma bayyana cewa, nadin ya fara ne a nan take.

Takardar ta kuma bayyana cewa, “Babban Kwamandan Askararwar Nijeriya, Muhammadu Buhari, GCFR, ya amince da nadin Mista Mohammed Bello-Koko a matsayin cikakken shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya nadin kuma ya fara a nan take”.

Kafin nadinsa, Bello-Koko Babban Darakta ne mai kula sashin kudi da gudanarwa na hukumar, yana kuma rike da mukamin ne tun da aka dakatar da Hadiza Bala Usman a kan wasu zarge-zarge da aka yi mata, duk da cewa, daga baya kwamitin ya wanke ta amma shugaban kasa yaga cancantar Mohammed Bello-Koko a matsyain wanda ya kamata ya jagoranci hukumar.

Wanene Mohammed Bello-Koko

An dai haifi Mohammed Bello-Koko a ranar 25 ga watan Maris na shekarar 1969 a karamar hukumar Koko-Besse ta Jihar Kebbi. Ya halarci Makarantar Sakandiren Gwmanatin Tarayya ta Sakkwato inda ya kammala a shekarar 1986. A shekarar 1992, ya kammala karatun Digirinsa a fannin Gudamnarwa a Jami’ar Usman Danfodiyo Sakkwato ya kuma zarce don yin digirin-digirgir a fanin Gudanarwa a shekarar 1995 duk a Jami’ar Usmanu Danfodiyo din.

Bello-Koko ya fara aiki ne da bankn ‘FSB International Bank Plc’ a garin Fatakwal ta Jihar Ribas a bangaren horas da ma’aikata. Daga nan ya kuma cigaba da samun daukaka a Bankin har ya kai matsayin mataimakin Babban Manaja.

Daga nan ne ya koma Bankin Zenith a shekarar 2005 a matsayin Babban Manaja mai kula bangaren manyan Kamfanoni, ya kuma zama Babban Manaja mai kula reshen Bankin na jihohin Ribas da Bayelsa ya kuma kasance cikin manyan masu gudanarwa a bankin na Zenith daga shekarar 2013 zuwa 2015 daga nan ne ya kama aiki a NPA a matsayin Darakta mai kula bangaren kudi da gudanarwa, a watan Mayu na shekarar 2021 ya kama aiki a matsayin mukaddashin Shugaban NPA daga na ne kuma aka nada shi mastayin shugaban Hukuma a ranar 15 ha watan Fabrairu na shekarar 2022.

Daga nada shi zuwa yanzu ya jaddada aniyarsa na kawar ayyukan rashin gaskiya a tashoshi ruwan kasar nan ya kuma yi alkawarin kyautata tsarin gudanar da ayyuka a NPA ta yadda zai yi daidai da abin da ake samu a kasashen duniya kamar dai yadda gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tsara, ya kuma nemi hadin kan dukkan masu suwa da tsaki a harkokin tashoshin jiragen ruwa su kawo nasu gudummawar don a tafi tare a tsira tare.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top