Riƙe Fasfo: Mabiya Shaikh Zakzaky Sun Cika Tituna A Jihohin Kaduna, Filato, Nasarawa Da Katsina

MMS HAUSA
0

Daga Muhammad Farouk

Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; Ƴan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun gudanar da muzaharori a jihohin Kaduna, Filato, Nasarawa, Katsina da kuma garin Jos ta jihar Filato domin ganin an saki ko sabunta fasfunan fita ƙasashen waje na Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddeen Ibrahim domin neman lafiyarsu da suka kwashe shekaru kusan bakwai suna fama da ita sakamakon harsasan dake jikinsu tun bayan harbin da sojoji suka yi musu a gidansu dake Gyallesu a cikin watan Disambar 2015 bayan kashe mabiyansa fiye da dubu. 

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International da kuma Kwamitin binciken kisan kiyashin mabiya Harkar Musuluncin, da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa, ya tabbatar da cewa an kashe tare da bizne gawarwaki 347 a ramin bai daya a Mando dake garin Kaduna. 

A garin Kaduna, wakilinmu ya labarto mana cewa muzaharar ta gudana ne daga Babbar Sabuwar Gadar Ahmadu Bello Way cikin tsakiyar garin da misalin karfe 3:00 na rana. Inda suke tafiya suna rera wakokin a saki fasfuna na Shaikh Zakzaky da matarsa. Muzaharar dai matasa ne zalla inji ganau, sannan kuma sun rufe ta a daidai Junction na Kano Road. 

Bayan Kammala muzaharar wakilinmu ya labarto cewa; daya daga cikin masu muzaharar ya bayyanawa al'umma cewa; "sun fito wannan zagaye ne domin ya zama jan kunne ga Gwamnatin Tarayya,  kan ta yi gaggawar sakar wa Shaikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenatuddeen Ibrahim fasfo dinsu domin su fia neman lafiya".

Irin waɗannan muzaharorin ya kuma gudana a garin Jos dake jihar Filato, garin Dutsin-Ma dake jihar Katsina da kuma Lafia ta jihar Nasarawa sai Zariya ta jihar Kaduna. 

Wakilinmu a Zariya ya aiko mana da rahoton cewa; a garin na Zariya ta jihar Kaduna gangami ne aka gudanar jim kadan da kammala sallar Juma'a a babban Masallacin Fadar Masarautar Zazzau. 

Haka daga garin Lafia ta jihar Nasarawa na nuni da cewa mabiya Shehin Malamin sun gudanar da irin wannan gangamin bayan sallar Juma'a. 

Bayanai sun nuna cewa yau kimanin watanni kusan Tara ke nan da wata Babbar Kotu a Kaduna ta wanke Shaikh Zakzaky da matarsa daga dukkanin tuhume-tuhume, inda ta ce ba shi da laifi, kuma ta ce a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba. 

Sai dai har yanzu gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta hana Shaikh Zakzaky da matarsa fasfo din su na fita ƙasashen waje domin neman lafiyarsu. Rahoton likitoci ya nuna cewa har yanzu akwai baraguzan harsashi a jikin Shehin Malamin da matarsa wanda hakan ke hana su walwala. 

Tuni Harkar Musulunci din ta maka bangaren Hukumar tsaro ta DSS, NIA da kuma Hukumar shige da fice ta Nijeriya wato Immigration a kotu inda take neman a saki ko a sabunta Fasfo din Shehin Malamin da matarsa. 
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top