Na Yafewa Kowa Da Kowa -Sakon Maryam Abacha Ga Al’umma

MMS HAUSA
0

Daga Ali Kakaki

Dr Maryam Sani Abacha, Matar tsohon shugaban kasar Nijeriya, Marigayi Sani Abacha, ta nemi dukkanin al’ummar da suka saba musu suka yi musu ba daidai ba, da wadanda suka yi musu abu mai kyau da maras kyau cewa; ta yafe musu baki daya, inda ta nemi al’umma da su dauki dabi’ar yafiya tare da yin alkhairi ga sauran al’umma.

Dr Maryam Sani Abacha ta bayyana hakan ne a birnin Tarayya Abuja, a yayin taron bikin taya ta murnar cika shekaru 75 a duniya wanda ya gudana a karshen watan Maris din nan.

Dr Maryam ta ce; “wani abu mai muhimmanci a rayuwa shi ne mu koyi yadda ake yafewa juna. Kuma mutane su yi kokari su rika yafiya. Yafiya yana da matukar muhimmanci. An karfafa a rika yin yafiya a harsuna daban-daban, da addini mabambanta, ba abin ya kai yafiya. Saboda yafiya kariya ne ga zuciya, kuma kariya ce ga rayuwa. Kuma yana nuna mutuncin al’umma”, ta lurantar.

Sannan ta ci gaba da cewa; “ina son amfani da wannan dama, ga mutanen da suke a nan, da wadanda ba su a nan, cewa; dukkanin abin da ya faru damu, mai kyau da mara kyau, mungodewa Allah bisa haka. Ina son kowa ya sani cewa; dukkanin mutanen da suka yi mana wani abu domin su taba ni, ina mai ba su hakuri, saboda Allah ya tsarkake zuciyata, kuma har yanzu ina raye, kuma nagodewa Allah. Ba abin mamaki bane na tafi a gobe, amma nagodewa Allah da rayuwata.

Ta ci gaba da cewa; “hakan ya faru ne ba wai saboda dabarata ba, sai bisa Rahamar Allah. Ga wadanda suka yi mana abubuwan rashin dacewa; ina son na yi amfani da wannan dama, na ce na yafe musu baki daya. Ba zan iya gaba da ku ba, kuma ban taba rike ku a zuciya ba. Na yafe muku baki daya, na yafe wa kowa da kowa. Da fatan duk zamu yafewa juna. Allah ta’ala ya yafe mana baki daya”, ta jaddada.  

Har wala yau duk a cikin jawabinta, Dr Maryam Sani Abacha ta yi wa kasa addu’a dangane da halin da kasar ta fada, inda ta ce Allah ya sa mu rayu cikin zaman lafiya a kasarnan. “Allah kuma ya daukaka kasarnan. Saboda ba ma cikin farin ciki a cikin kasarmu, abin bakin ciki ne bisa dukkanin abubuwan da suke faruwa saboda mu, mu mutanen kasarnan”.

Ta kuma nemi shugabanni da mabiya dukkansu su ji tsoron Allah a kuma yafe wa juna; “ sannan a kuma yi abubuwan alkhairi a tsakani. Kamar yadda muka dan yi da karamin abin da muke da shi. Idan kowa zai bada na shi gudummawar ga dukkanmu, tabbas sakayyar zai zama a mafi kyawun wuri. Mu zama mutanen kirki, masu dabi’ar yafiya da mantuwa, kuma mutanen kirki; Allah ya yi wa Nijeriya albarka. Allah ya albarkaci wannan al’umma, Allah ya yi mana albarka.

“Mungode sosai bisa soyayyar da kuka nuna mana, bisa komai da komai. ‘ya’yana da iyalina, nagodewa kowa da kowa”, ta karkare.
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top