Domin dacewa da falalar watan Ramadan mai girma, don kuma sauƙaƙawa al'ummar musulmi sauraron karatuttukan Tafsirin Alkur'ani mai tsarki.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, kuma tsohon gwamna Jihar Kwara Dr. Abubakar Bukola Saraki ya ɗauki nauyin sa karatun Tafsiri a gidajen rediyo kamar haka:
1. Sashen Hausa na Rediyon Tarayya FRCN
- Tafsirin Sheikh Abdullahi Bala Lau
LOKACI: 8:00pm - 8:30pm
2. Gidan Rediyon Nagarta
- Tafsirin Sheikh Dahiru Usman Bauchi
LOKACI: 6:30am - 7:00am
3. Gidan Rediyon Rahama dake Kano
- Tafsirin Sheikh Karibullah Nasiru Kabara
7:30pm - 8:00pm
4. Gidan Rediyon Vision FM Kano
- Tafsirin Sheikh Jafar Mahmud Adam
LOKACI: 7:00am - 8:00am
5. Gidan Rediyon Caliphate dake Sakkwato.
- Tafsirin Farfesa Mansur Sokoto
LOKACI: 7:00pm - 7:30pm
Sannan a lokaci guda kuma ya ɗauki nauyin kiran sallah a gidajen rediyo don mutane su kiyaye lokutan da za su daina yin sahur, da kuma lokutan buɗa baki.
Ana sanya wannan kiran sallah ne a gidajn rediyo kamar haka:
1. Gidan Rediyon Freedom
2. Gidan Rediyon Nagarta
3. Gidan Rediyon Rahama dake Kano
4. Gidan Rediyon Vision FM dake Kano
5. Gidan Rediyon Caliphate dake Sakkwato.