Ƙungiyar Kare Muradun Dimokraɗiyya 'Northern Democratic Defence League' ta yaba wa Dattawan Arewa bisa fidda 'yan takarar maslaha daga yankin Arewa.
Ƙungiyar ta NDDL ta bayyana haka ne a wata takardar manema labarai da shugabanta, Auwal Liti Darazo ya sanya wa hannu yau a garin Kaduna.
Idan dai ba a manta ba, a jiya Juma'a ne Ƙungiyar Dattawan Arewa karkashin jagorancin, Farfesa Ango Abdullahi suka fitar da sanarwar sakamakon fitar da ɗan takarar maslaha na shugaban ƙasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
Kungiyar ta dattawan Arewa ta ce, bayan gudanar da jin ra'ayin shugabanni daga yankin arewa, sun samar da sakamakon da ya fiddo Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki da gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad a matsayin 'yan takarar maslaha.
Inda Ƙungiyar ta dattawan Arewa ta nemi mutum biyun su yi sulhu tsakaninsu wurin aminta da takarar mutum ɗaya.
Kungiyar ta dattawan Arewa ta ce, 'yan takarar shugaban ƙasa hudu daga arewa ne suka haɗu wuri ɗaya domin fitar da mutum ɗaya cikinsu. 'Yan takarar sune; Abubakar Bukola Saraki, Aminu Waziri Tambuwal, Bala Mohammed da Mohammed Hayatuddeen. Inda suka nemi dattawan arewan su yi bincike su kuma fitar da ɗan takarar maslaha.
Kungiyar Kare Muradun Dimokradiyya ta ce, abin farin ciki ne da murna ganin yadda dattawan Arewa suka gudanar da aikin tantancewa tare da fitar da waɗannan 'yan takara. "Muna sa ran za su zauna su fahimci juna, sannan su fitar da mutum ɗaya a cikinsu." Inji kungiyar