Muna Alfahari Da Farfesa Gwarzo Bisa Kafa Jami'o'in Da Ya Sanya Sunan Mahaifiyarmu -Muhammad Abacha

MMS HAUSA
0

Muhammad Sani Abacha, Babban dan Marigayi Janar Sani Abacha, ya yabawa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa kafa jami'o'i a jamhuriyar Nijar da Nijeriya tare da sanya sunan mahaifiyarsu, Maryam Abacha.


Farfesa Gwarzo shi ne wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Maradi a Jamhuriyar Nijar da kuma ta Kano a Nijeriya.

Abacha, wanda ya tsaya takarar gwamnan Kano a shekarar 2015, ya bayyana hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Tarayya Abuja a ranar Laraba.

A cewarsa, iyalan Abacha suna alfahari da Farfesa Gwarzo bisa karramawar da ya yi wa mahaifiyarsu ta hanyar sanya wa jami'arsa (Maryam Abacha American University ta Nijer da kuma Kano a Nijeriya) sunan mahaifiyarsu a bar kaunarsu, Maryam Abacha.

“Muna alfahari da Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da ya kafa jami’ar a Jamhuriyar Nijar da kuma nan Kano wadda ya sanya wa sunan mahaifiyarmu.

“a kashin kaina ina matukar farin ciki da kuma alfahari da Farfesa Gwarzo wanda na dauke shi a matsayin kanina. Ba mu da isassun kalmomi da za mu gode tare da yaba masa da kuma nuna jin dadinmu kan wannan karamcin da ya nuna mana,” in ji Abacha.

Ya kuma jinjinawa Farfesa Gwarzo bisa jajircewarsa wajen inganta ilimi ba a Nijeriya kadai ba har ma a Afirka baki daya.

“Ko a kwanan baya wasu mutanen Ghana sun bukaci shi (Farfesa Gwarzo) ya kafa irin wannan jami’a a birnin Kumasi na kasar Ghana. Wannan abin farin ciki ne a ce al’umma daga wasu kasashe suna neman wani abu makamancin haka,” inji shi.

Abacha ya kuma sake jaddada yabonsa ga Farfesa Gwarzo kan wannan shirin domin a cewarsa, yankin arewacin kasar nan an bar shi a koma ta fuskacin ilimin zamani.

“Akwai dalibai da dama da aka yaye daga Jami’ar MAAUN, kuma a halin yanzu suna aiki a wurare daban-daban a fadin Nijeriya da waje,” in ji Abacha.

Ya nusasshe da cewa jami’o’in za su bai wa matasa da dama damar samun ilimi mai inganci kwatankwacin na Turai wanda hakan zai bai wa wadanda suka kammala karatunsu damar yin gogayya da sauran wadanda suka kammala jami’a a fadin duniya.

Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da bai wa Farfesa Gwarzo kwarin guiwa da jajircewa wajen ganin ya yi iya bakin kokarinsa wajen samar wa da dalibai ingantaccen ilimi domin su ba da ta su gudummawar wajen habbaka tattalin arziki da ci gaban nahiyar Afrika baki daya.

Ya kara da cewa; “Muna fatan ganin an kafa karin jami'o'i kamar 10 zuwa 20 nan da 'yan shekaru masu zuwa.”
Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top