Hukumomi a ƙasar na zargin mazajen nasu ne da taimaka wa ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta Boko Haram ta hanyar yi musu canjin kuɗin ƙasar waje.
Mafi yawan mazajen da ake tsare da su fiye da shekara ɗaya 'yan kasuwar canji ne da aka fi sani da wapa, kuma tun da aka kama su ba a bari iyalansu sun gan su ba in ban da kwanan nan, a cewar matan.
Matan ƙarƙashin jagorancin Aisha Jibril sun ce "buƙatarmu ita ce a gurfanar da su a gaban kotu, masu laifi a hukunta su, waɗanda ba su da laifi a sako mana mazajenmu".
Wasu daga cikin matan sun fito ne tare da 'ya'yansu ƙanana maza da mata.
A 2021 ne wata kotu a Dubai da ke ƙasar Daular Larabawa (UAE) ta yanke wa wasu 'yan Najeriya hukunci, ciki har da ɗaurin rai-da-rai, saboda kama su da laifin yi wa Boko Haram canjin kuɗaɗe.
Sakamakon haka ne jami'an tsaro a Najeriya suka fara kamen wasu 'yan canjin da ake zargi da tallafa wa ƙungiyar wajen yi musu safarar kuɗaɗe.