Masu Zuwa Maulidi Zamfara: Duk Wanda Dare Ya Yi Masa Akwai Masauki A Funtuwa -Zawiyyar Sheikh Alti

MMS HAUSA
0

 


Daga Hussaini Yero

A yanzu haka taron maulidin Sheikh Ibrahim Inyass, Kalifan Shehu Ahmadu Tijjani karo na 36, ya kankama dan dubban mutane ke ta shigowa daga sassan kasarnan dama wajenta, akan haka ne Zawiyyar Sheikh Abubakar Alti Funtua karkashin Jagoranci, Khalifa Ali Sa'idu Alti Funtua ya ke sanar da matafiya cewa, duk wanda shida da rabi ya yi masu a Funtuwa su tsaya su kwana akwai masauki saboda matsalar 'yan fashin daji.

Khalifa Ali Saidu Alti Funtua ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a dakin taron makon Shehu da ake ci haba da gudanar da shi a Gusau.

Khalifa ya bayyana cewa, Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass karo na 36, da yanzu haka ya ke gudana a nan Gusau; wajibin mu ne mu bada gudunmulawar mu wajalen ganin bakin Shehu ba su samu matsala ba wajen shigowa Gusau, a don haka mu ka tanadi masaukai a garin Funtua dan kauce ma tafiyar dare. "don haka duk wadanda suka yi dare su je Zawiyyar Sheikh Abubakar Alti Funtua dan ya da zango, washegari a shigo Gusau. Fatanmu shi ne Allah ya kawo kowa lafiya ya kuma maida mu gidajaemu lafiya".

A ranar Asabar ne za a kammala wannan gagarumin Taron maulidin Sheikh Ibrahim Inyass karo na 36 a Zamfara, wanda yanzu haka 'ya'yan Sheikh Ibrahim Inyass daga Kaulaha tuni suka iso Zamfara wajen maulidin.

Tags

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top